Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da cewa za ta kammala zangon karatu na 2019/2020.
Wannan na dauke ne cikin wata sanarwa da Magatakardar Jami’ar Fatima Binta Mohammed ta sanya wa hannu.
- Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki
- ASUU da Gwamnati sun daidaita
- ASUU za ta bude jami’o’i a watan Janairu 2021 —Minista
- Sabon Shugaban Jami’ar Bayero ya kama aiki
Sanarwar ta ce ranar 18 ga Janairu 2021, ita ce ranar da za a fara kashin farko na zangon karatun 2020/2021.
Sannan kashi na biyu na zangon karatun zai fara ranar 3 ga watan Mayu, 2021.
Su kuwa masu karatun gaba da digirin farko, za su fara karatu ne a ranar 18 ga watan Janairu 2021, a matsayin kashin farko na zangon karatunsu a bana.
Sai kashi na biyu na zangon karatun na su zai fara ranar 1 ga Yuni, 2021.
Majalisar Gudanarwar Jami’ar ta umarci daliban gaba da digirin farko da ba su yi rajista a kan lokaci ba a baya, da su yi kafin lokaci ya kure musu.
Kazalika, Majalisar Gudanarwar Jam’iar ta sauya wa zangon karatun 2019/2020 zuwa 2020/2021.
Idan ba a manta ba kungiyar malaman jami’o’i ta kasa ASUU ta shiga yajin aiki a ranar 23 ga Maris, 2020, sannan ta janye yajin aikin a ranar 22 ga Disambar 2020.
Yajin aikin da ya dauki tsawon watanni tara, lamarin da ya janyo tangarda a jadawalin tsarin karatun jami’o’in kasar nan kuma haka ya sanya Jami’ar ta yanke hukuncin soke zangon karatun tare da fara sabo.