Jam’iyyar APC na shirin gyara kundin tsarin mulki ta yadda za ta tilasta wa zababbu da masu rike da mukaman siyasa ganawa da jama’ar rumfunan zabensu sau biyu a shekara gabanin zaben 2023.
Wakilin matasa a kwamitin rikon jam’iyyar na kasa, Barista Ismaeel Ahmed yayin ganawa da wakilan matasan jam’iyyar na jihohi ya ce ya gabatar wa Shugaba Buhari da sauran shugabannin jam’iyyar shawarar yin hakan.
“Wannan zai ba wa mutanenmu a mazabu da gundumomi kwarin gwiwa game da jam’iyya da shugabanninta.
“Zai wayar da kan ‘yan jam’iyya da ke gundumomi game manufofi da ayyukan gwamanti.
“Na tattauna da Shugaban Kasa kuma ya yi na’am da hakan ina kuma kyautata zaton zai samu amincewa a kundin tsarin jam’iyya.
“Lokaci ya yi da shugabannin za su rika komawa gundumomi suna ganawa da ‘yan jam’iyya duk bayan wata shida.
“Ka yi tunanin tasirin da za a samu idan Shugaban Kasa ko Shugaban Majalisar Dattawa ko Gwamna ko Minista na halartar taro a mazabunsu.
– Kara damawa da matasa a jam’iyya –
“Mun bayar da muhimman shawarwarin sauye-sauye a tsarin mulkin APC da za a bi a babban taro da zaben fitar da ‘yan takara, wanda muka yi amannar zai kara shigo da matasa a cikin harkokin gudanar da siyasa.
“Mun kuma duba yiwuwar gabatar da daftarin Manufofin Matasa na APC a shigar da su a cikin manufofin jam’iyyar da za su biya bukatun matasa”, inji shi.
“Jam’iyyarmu na da mutum miliyan 15 wadanda daga cikinsu mutum miliyan 11 matasa ne, kuma ya kamata a ba su muhimmanci
“Matasa ne masu jam’iyyar amma duk da cewa akwai wasu majalisu a jam’iyya, muna neman a yi wa tsarin jam’iyya gyara domin a samar da majalisa mai karfi ta matasa”, inji shi.