Jam’iyyun APC da PDP a Jihar Sakkwato suna cacar baki kan zargin da ake yi na akwai wani shiri na kone ofishin Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke jihar.
Da farko APC ce ta fitar da bayanin shirin kone hukumar, inda ta nuna shiri ne na marasa kishin kasa.
Bayanin APC dauke da sa hannun Kakakin Jam’iyar, Alhaji Sambo Bello Danchadi da aka raba wa manema labarai a Sakkwato ya ce, “Ana so a sanya wutar ce don a kawar da duk hujjojinmu da za mu kai gaban kotun sauraren karar zaben Gwamna da ke zamanta a Sakkwato.”
Haka bayan APC ta jawo hankalin jami’an tsaro kan su tabbatar da tsaro a ofishin Hukumar INEC na jihar, ita ma PDP ta yi wannan kira har ta nuna damuwarta kan kalaman APC na shirin kona ofishin.
A wata takarda da shugaban Jam’iyyar PDP Alhaji Ibrahim Milgoma ya fitar ya ce wannan zargin da ake yi ya kamata hukumomin tsaro su tashi tsaye.
“Wannan ba abin wasa ba ne ganin yadda maganar zabe take gaban kotu, ba wai jami’an tsaro su tsaya su ji ba, kamata ya yi su zauna a shirye wajen kare ofishin, kuma su binciki inda APC ta samu labarin.”
Zargin da APC suka yi ya zo bayan kwana shida da kotu ta ba su damar duba kayan zaben da aka yi amfani da su zaben bana.