✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘APC ba ta san darajar mutanen Sokoto ba’ —Milgoma

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta ce jam’iyyar adawa ta APC ba ta san darajar mutanen Sakkwato ba. Jam’iyyar ta PDP ta fadi hakan ne…

Jam’iyar PDP a jihar Sakkwato ta ce jam’iyyar adawa ta APC ba ta san darajar mutanen Sakkwato ba.

Jam’iyyar ta PDP ta fadi hakan ne yayin da take mayar da martani ga APC a kan takardar da ta fitar tana kalubalantar gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da cewa ba ta aiwatar da komai ba a cikin shekaru biyar.

A wata takarda da aka raba wa manema labarai a Sakkwato, wadda shugabanta a jihar,  Alhaji Ibrahim Milgoma, ya sanyawa hannu, jam’iyar PDP ta musanta jawaban da takwararta ta APC ta yi.

“A lokacin da sauran takwarorinsa ke cikin bukukuwan murnar cika shekara daya a karo na biyu na mulkin su, wato shekaru biyar ke nan a jumlace, shi kuma Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tsintsi kansa a wani yanayi wanda ya sa dole ya kama hanya zuwa Abuja don magance matsalar.

“Babban burinsa shi ne ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari don sanar da shi yadda ‘yan bindiga da masu satar mutane ke cin karensu ba babbaka da rayukan mutane da dukiyoyin su a karamar hukumar Sabon Birni dake Sakkwato”, inji sanarwar.

Fannin tattalin arziki

Milgoma ya ce Tambuwal ya tsaftace fannin kula da kudi da ke cike gibi da manyan beraye; ya gano ma’aikatan bogi da wasu manyan APC ke amfana da su, lamarin da ya yi sanadin karbo miliyoyin nairorin jama’a.

“Ya samar da sabon tsarin zamani na tattara haraji wanda ya samu karbuwa a ciki da wajen jiha, inda ya soma seta tattalin arzikin jiha da manyan berayen APC suka lalata.

“Hakan ya ba shi damar samar da kudade Naira biliyan hudu don tallafa wa jama’a masu karamin karfi da kudi N20,000 ko wanne, a dukkan kananan hukumomi 23 na jiha don soma kananan kasuwanci.

“Haka ma Gwamna ya gina sabon bankin al’umma don samar da bashi mai sauki ga jama’ar jihar Sakkwato, inda shi ma Naira biliyan biyu tuni suka shiga hannun mutane.” A cewar shugaban jam’iyar ta PDP.

Shugaban jam’iyyar ta PDP ya kuma soki APC yana zarginta da nuna halin ko-in-kula da halin da mutanen jihar ke ciki.

“Saboda rashin ganin darajar rayuwar jama’a…da son kowa ya yi biris da iftala’in da Sabon Birni da sauran kananan hukumomi a Sakkwato suka shiga, sun mai da hankalinsu ga jawabin da Gwamna Aminu Waziri Tambuwal zai yi na irin dimbin ayyukan da aka yi a kowane sako da lungu na jihar Sakkwato wanda su ‘yan adawar suka zamo makafi a kai.” inji shi.

‘Kulle-kulle da zagon-kasa’

Ya kuma ce duk da kulle-kulle da zagon kasa da APC ke ci gaba da yi wa Gwamna Tambuwal, har yanzu bai yi kasa a gwuiwa ba wajen sauke nauyin da Allah ya dora masa na jagorancin jihar Sakkwato.

“Duk da irin dabaibiyar da APC a Sakkwato ta saka ma Gwamna Tambuwal, da kuma karancin kudaden shiga da Sakkwato ke fama da shi, ya samu gina makarantu, hanyoyi da samar da kiwon lafiya a duk fadin jiha.

“Saboda ma irin hobbasa da ya yi a fannin ilmi, ya samu lambobin yabo da karramawa daga ko ina ciki da wajen jiha”, in ji shi.

Tun da farko dai jam’iyar ta APC ce ta zargi gwamnatin Aminu Waziri Tambuwal da kasa aiwatar da wani abin-a-zo-a-gani a tsawon shekara biyar.

‘Ba romon dimokuradiyya’

A cewar jam’iyar ta APC, hakan ne ya sa wasu magoya bayan jam’iyar PDP a jihar dawowa daga rakiyar gwamnatin domin ta kasa samar da walwala ta romon dimukuradiyya ga magoya bayanta, ba a maganar Sakkwatawa gaba daya.

Shugaban APC Alhaji Isah Sadik Acida ne ya furta kalaman a wata takarda da jam’iyar ta fitar aka rabawa manema labarai a Sakkwato, yana cewa sun saba idan gwamnati ta cika watanni 12 takan yi bayanin abin da ta yi domin a gani a kasa, amma a jihar Sakkwato ta yi gum da bakinta kamar Mallam ya ci shirwa.

“Duk da haka dai ba mu yi mamaki ba, saboda sabanin sauran jihohi, jihar Sakkwato kam babu abin a-zo-a-gani na romon dimokradiyya.” a cewarsa.

Bullar Coronavirus

Ya kara da cewar akwai yiyuwar gwamnatin Sakkwato ta labe bayan matsalar annobar coronavirus a matsayin uzurin kasa samar da wani aikin ci gaban al’umma.

“A fili take cewa coronavirus ta bayyana a jihar Sakkwato a watan uku na wannan shekarar ta 2020 sannan duk gwamnan da ke son kawo wani aikin ci gaban jama’a ya riga ya gama shi.

“Tun bayan zaben Gwamna Aminu Waziri Tambuwal a jihar Sakkwato mai cike da sarkakiya, gwamnatin Sakkwato ta kasa aiwatar da ko tsara wani aikin raya al’umma domin fitar da Sakkwato cikin kangin talauci.

“Hakan ya sanya hukumar kula da kididdiga ta kasa ta bayyana cewa Sakkwato ita ce ta farko a jerin jihohin kasar nan da suka fi talauci”, in ji shi

Ya ce abin da kawai aka sani ga gwamnatin Sakkwato shi ne, “Za mu yi” – “alkawarin da bai karewa kuma ya zama gafara sa ba mu ga kaho ba.”