Kungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru da ke alaka da Al-Qaeda a Arewa maso Yammacin Najeriya, ta musanta hannunta a kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ranar 28 ga watan Maris din 2022.
Harin ya yi sanadin mutuwar akalla mutum tara tare da raunata wasu damma yayin da kuma aka sace wasu.
- Neman gurbin AFCON: Najeriya ta lallasa Sao Tome and Principe da ci 10-0
- Yajin aiki: ASUU ta lashi takobin hukunta jami’o’in da suka bijire mata
Ansaru ta karyata zargin hannunta a kai harin a wani bidiyo da ta saki a ranar Lahadi a Telegram da RocketChat.
Mai magana a cikin bidiyon ya yi jawabin cikin harshen Larabci da kuma Hausa.
Akalla mutum bakwai ne suka bayyana a bidiyon kowanensu dauke da bindiga kuma fuskarsa a rufe.
Mai magana a bidiyon ya ce “Labarin karya da ya ke yaduwa cewa kungiyar Ansarul al-Muslimin fi bilad al-Sudan ta dauki alhakin kai harin jirgin kasan.”
“Wannan karya ce tsagwaronta wacce ba ta da tushe.”
Ya ce Ansaru ba ta da hannu ko kadan a harin jirgin ko sace fasinjojinsa.
Sai dai hukumomi a Najeriya sun zargi Ansaru da kuma Boko Haram da hannu a kai wa jirgin kasan hari.
A baya-bayan nan wanda suka kai harin sun kuma sakin bidiyo da hotuna na mutanen da suka sace a jirgin tun bayan harin.
MSai dai mai magana a madadin kungiyar ta Ansaru ya ce an tsara labarin karyar ne don a zubar musu da mutunci.
Kazalika, ya jaddada cewa kungiyar na kokarin kaucewa cin zarafin ‘yan yankin kuma tana taba wadanda suke adawa ko fito-na-fito da ita ne kawai.