Annobar cutar Coronavirus ta sake barkewa karo na uku a Jihar Legas kamar yadda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar a ranar Lahadi.
Cikin sanarwar da ya fitar a Fadar Gwamnatinsa da ke birnin na Ikko, Sanwo-Olu ya ce za gwamnatinsa za ta yi duk wata mai yiwuwa wajen takaita yaduwar cutar.
Ya yi kira ga mazauna jihar da su mutunta dokokin da aka kafa domin yaki da annobar, a yayin da ya yi barazanar daure bakin da suke shiga jihar ta jiragen sama ba tare da bayar da lambobin wayar su ba domin sanin inda suke inda bukatar hakan ta taso.
A jawabin da ya gabatar, Gwamnan ya ce, “ya zama wajibi na yi wa al’umma bayanin halin da ake ciki da kuma matakan da muke dauka a hukumance domin kare lafiyar al’umma.
“Duk da dabarun da muka samar na dakile cutar a cikin watanni uku da suka gabata, abin takaici bayan al’amura sun fara komawa daidai yadda mutane suka fara gudanar da rayuwarsa ta yau da kullum, yanzu haka jihar ta samu kanta a yanayi na dawowar cutar a karo na uku.”
Gwamnan ya bukaci al’ummar jihar da su mutunta dokokin da aka tanada, inda yake cewa Najeriya baki daya na bukatar ganin Jihar ta dakile yaduwar cutar domin zaman lafiyar kasar baki daya.
Sanwo-Olu ya ce zasu ci gaba da yin gwaji ba tare da kaukautawa ba da kuma mayar da hankali kan samfurin da suke dauka daga jama’a domin gano irin nau’in cutar da kuma mutanen dake dauke da ita.
Gwamnan ya ce ta hanyar gwaji ne kawai za’a iya daukar matakan dakile cutar, yayin da ya gargadi jama’a da su kaucewa zuwa wurin masu gwaji na bogi.
Dangane da maganin rigakafi kuwa, Sanwo-Olu yace ya zuwa yanzu kashi guda ne kawai na mazauna birnin suka karbi allurar sau biyu, abinda yake cewa ya gaza a yunkurin da suke na dakile mutuwar da annobar ke haifarwa.
Gwamnan ya bayyana damuwa cewar, daga fasinjojin jiragen sama da suka shiga kasar daga ranar 8 ga watan Mayun bana zuwa 7 ga watan Yuli dubu 50 da dari 322, basu gano kashi 18 daga cikin su domin tantance halin lafiyar sub a saboda gabatar da adireshi na bogi.
Sanwo-Olu, ya kuma bukaci shugabannin addinai da su ci gaba da mutunta dokokin da aka shimfida na rage cinkoso domin kare lafiyar jama’ar su musamman a wannan lokacin da ake fuskantar bikin Sallar Layya.