kungiyar ’yan asalin wasu Jihohi mazauna Jihar Oyo (ANIRO) ta gargadi ’ya’yanta kada su kyale ’yan siyasa su yi amfani da su wajen cim ma buri a zaben badi.
Shugaban kungiyar na kasa Dakta Camillus Asumu ne ya yi wannan gargadi a Ibadan cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawun kungiyar Mista Joseph Ogunleye ya sanya wa hannu a ranar Litinin.
Dakta Carmillus Asumu, wanda ya jagoranci shugabannin kungiyar zuwa ziyarar ofisoshin shiyyoyi domin ganawa da ’yan kungiyar da ke zaune a kananan hukumomi 33 a Jihar Oyo, ya ce, ya gano jam’iyun siyasa a Najeriya sun kware wajen yin amfani da kungiyoyi domin cim ma burinsu, sannan su yi watsi da su bayan sun yi nasara, don haka babu ruwan ANIRO da harkokin siyasa.
“A dalilin haka ne ANIRO ta fara ganawa da ’ya’yanta domin ilmantar da su illar da ke tattare da zama karen farautar jam’iyun siyasa. Yanzu haka mun gano wasu mutane da suke yi wa kungiyar mu sojan gona da suke zuwa wurin ’yan siyasa suna mika sunayen karya domin karbar kudade a hannunsu. Muna sanar da jam’iyyu da ’yan siyasa babu ruwan kungiyarmu da al’amuran da suka shafi siyasa.” Inji shi
Ya bukaci shugabannin kungiyar na shiyyoyi su tashi tsaye wajen yin bincike don bankado irin wadannan mutane, sannan su mika su ga jami’an tsaro domin shawo kan matsalar.
Ya bayyana farin cikinsa a kan irin hadin kan da uwar kungiyar take samu daga shugabannin shiyyoyi, sannan ya nemi ’yan kungiyar su kasance masu bin doka da oda da girmama zamantakewa tsakaninsu da jama’ar garuruwan da suke zaune a matsayin baki.
Ya kuma yi wa manoma daga cikin ’yan kungiyar albishirin samun garabasar horo kyauta da shawarwarin da za su taimaka wajen bunkasa harkokin noma wanda cibiyar binciken harkokin noma a kasashe masu zafi IITA da ke Ibadan za ta dauki nauyin gudanarwa.
Da yake zantawa da Aminiya, daya daga cikin shugabannin (ANIRO) na kasa Alhaji danjuma Garba Garas, cewa ya yi, “mun yi kwanaki 3 muna zagayawa zuwa sassa daban-daban na Jihar Oyo, domin wayar da kan manbobin kungiyarmu a game da kyautata zamantakewa a tsakaninsu da jama’ar garuruwan da suke zaune.”