Mutane da dama sun shiga kaduwa da jimami bayan samun labarin rasuwar Sani Ruba, wani matashin da ke shirin angwancewa a ranar 11 ga watan Disamban 2021.
Yana dai shirin angwancewa ne da fitacciyar ’yar kasuwar kafar sada zumunta ta zamanin nan, Rafeeah Zirkarnain.
- DPO ya lashe musabakar Alkur’anin ’yan sanda ta farko a Kano
- Sanya takunkumi ya fi rigakafi zama kariya daga COVID-19 – Sabon bincike
Masoyiyar mamacin ce ta fara wallafa labarin rasuwarsa a shafinta na Facebook, da misalin karfe 7:00 na daren ranar Alhamis.
“Innalillahi wa Inna ilaihir raj’iun masoyi Sani Ruba ashe ba za mu kasance mata da mijin ba a ranar 11 ga Disamba….. Tun jiyan nake jin wani yanayi a raina amman na rike tunanin a raina… Ba zan taba samun mutum irinka a matsayin miji ba,” kamar yadda ta wallafa a shafin nata na Facebook.
Sani, mai shekara 36 a duniya, dan asalin garin Ruba ne da ke Jihar Jigawa, wanda yanzu yake zaune a garin Jos na Jihar Filato.
Rahotanni sun ce matashin angon ya gamu da ajalinsa ne, a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a kan titin Numan zuwa Gombe, a ranar Alhamis.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin amaryar, amma hakan ya ci tura saboda ta gaza daukar wayata ko amsa sakon kar-ta-kwanan da ya tura mata, sboda kaduwa da dimuwar da take ciki.
Kafin rasuwarsa, marigayin ya yi karatu a Sashen Koyar da Aikin Jarida na Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK).
Tuni dai mutane da dama, ciki har da malamansa na jami’ar, suka shiga nuna alhininsu tare da mika sakon ta’aziyya ga iyaye, abokai da kuma amaryar tasa wadda mutuwa ta yi musu yankan-kauna.