✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ango ya yi karar amaryarsa yana namen N10m kan ruwan sanyi

Ango na neman amaryarsa ta biya shi Naira miliyan 10 bayan ta sheka masa ruwan sanyi

Wani ango a Kano ya garzaya kotun Musulunci yana neman amaryarsa ta biya shi Naira miliyan 10 saboda ta antaya masa ruwan sanyi.

Migadancin ya kuma nemi kotun ta raba aurensa da amarya tasa saboda abin da ta yi masa don ya hana at kudin da ta  nema daga gare shi domin shirya bikin zagayowar ranar haihuwarta.

A yayin gurfanar da amaryar a kotun da ke zamanta a titin Post Office, angon ya shaida wa alkali cewa ruwan sanyin da ta sa ta sheka masa ya yi sanadin kamuwarsa da rashin lafiya.

’Yan sanda sun gurfanar da matar ce a gaban Mai Sharia Nazifi Adam kan zargi uku na tauye hakkin dan Adam, yaudara da kuma cin amana.

Lauyan mijin, Badamasi Gandu, ya bayyana wa alkali cewa bayan amaryar ta nemi angon ya ba ta kudin shirya bikin zagayowar ranar haihuwarta, sai angon ya ki, wanda hakan ya fusata ta har ta ta ji wa mijin rauni ta kuma nemi ya sake ta.

Lauyan ya shai dawa kotun cewa, muddin amaryar na son rabuwa da mjiin nata, to dole ta biya shi Naira miliyan 10 da ya kashe a kan aurenta.

Sai dai da aka karanto mata tuhume-tuhumen, wadda ake zargin at musanta.

Daga baya alkalin ya ba da belin ta bisa hujjar cewa har yanzu matar mai karar ce, sannan ya dage sauraron shari’a zuwa ranar 3 ga watan Maris.