Da alama tirka-tirkar da ke tsakanin tsohon dan Majalisar Wakilai daga Jihar Jigawa, Honarabul Usaini Namadi da amaryarsa Jamilah Ahmad Sanusi ta zo karshe sakamakon sakinta da tsohon dan majalisar ya yi a shekaranjiya Laraba.
Da yake tabbatar wa Aminiya aukuwar lamarin ta talho, Lauya mai kare Jamilah Ahmad Sanusi da kuma matar da ta yi hanyar auren, Barista Sa’id Tudun Wada, ya ce mai karar ya yi wa amaryar saki daya tak kuma ma har ya aika mata da takardar sakin.
Tudun Wada ya ce ga dukan alamu lamarin ya zo karshe domin da zarar an koma kotu a ranar 15 ga Maris mai zuwa, mai karar zai janye karar kuma ya shaida wa kotun cewa ya saki Jamilah.
“Ka san a zaman kotu na karshe mun roki a bari mu sasanta a wajen kotu. To a gaskiya mun cimma nasarar zaman namu. Kuma yanzu haka Honarabul ya saki matar tasa saki daya har ma ya aika mata da takardarta ta saki. Don haka ga alama karar ta zo karshe,” inji Tudun Wada.
Binciken da Aminiya ta yi ya tabbatar da cewa Honarabul Namadi mutumin kirki ne wanda ba ya son fitina ko kadan don haka ma bayan da labarin tserewar amaryarsa ya bayyana, gidan Honarabul din da ke Nassarwa GRA a birni Kano, ya zama tamkar gidan zaman makoki domin juyayin wannan lamari da ya faru.
Majiyar Aminiya ta gano cewa Honarabul Namadi da iyalinsa sun shiga matsanancin halin damuwa da takaici sakamakon aukuwar lamarin da irin tereren da aka yi da labarin ta gidajen jaridu da kafafen sadarwar zamani.
Wakilinmu ya gano cewa ba tsohon dan majalisar ne ya kai karar Jamilah da mai dalilin auren ba, bincike ya nuna cewa wani amininsa ne da ya yi uwa ya yi makarbiya a harkar auren ya shigar da karar a kotu domin karbo masa hakkinsa.
Haka Aminiya ta gano cewa, duka-duka abin da tsohon dan majalisar ya kashe a auren bai wuce Naira miliyan biyar ba, sabanin yadda aka baza labarin cewa ya kashe sama da Naira miliyan 30.
A makon jiya ne labarin amaryar dan majalisar kuma wanda ya nemi tsayawa takarar Gwamnan Jihar Jigawa ya watsu a kafafen watsa labarai da na sada zumunta cewa ya yi karar amaryarsa da mai dalilin aurenta a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Shahuci a Kano kan guduwa daga gidansa bayan ya kashe Naira miliyan 30 a aurenta.
Lauyan mai kara Barista Ukashatu Adamu ya shaida wa kotu cewa tsohon dan Majalisar Wakilan na mazabar Hadeja da Auyo da Kafin Hausa a Jihar Jigawa ya bayar da kwangilar a sama masa mata ce a Jamhuriyyar Nijar “matar ta kasance fara doguwa mai kyan diri.”
Bayan an samo amarya mai suna Jamila dawainiyar bikin da hada-hadar jigilarta da danginta daga Nijar zuwa Najeriya ta lashe Naira miliyan 30, don haka ya nemi kotu ta tilasta matarsa dawowa dakinta ko a dawo masa da kudin da ya kashe Naira miliyan 30.
Sai dai lauyan Jamila, Barista Sa’idu Tudun Wada ya nemi mai kara ya janye sunan mai dalilin aure saboda ta sauke nauyinta na samo macen da yake so, bukatar da alkalin kotun Mai shari’a Garba Ahmed ya ki amincewa da ita.
Lauyan ya kuma nemi kotu ta ba su damar yin sulhu kuma ya yi wa angon tayin auren kanwar Jamilar da ya ce tana da siffofin da Jamila ke da su a cewarsa har ma ta fi ta kyau.
Lauya Ukashatu ya kuma ce hoton da ake ta yadawa a kafafen sada zumunci ban a amaryar ba ce. “Mun ga ana ta yada hotuna a kafafen sada zumunci, muna sanar da jama’a cewa wannan ba hoton amaryar ba ce, na wata matar aure ce daban wadansu suka dauko suka hada da na mai kara.”
Aminiya ta gano cewa matar da aka hada hotonta da na dan majalisar matar wani fitaccen mutum ne a Kano da yanzu haka take zaune a dakin mijinta da kuma ’ya’yanta.