Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta kama wani mutum mai shekara 30, kan zargin sa da kashe amaryarsa mai shekara 25.
Kakakin rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN), a ranar Asabar.
- Obi ya girmi Kwankwaso a fagen siyasa — Bashir Ahmad
- Da jami’an gwamnati nake zuwa tattaunawa da ’yan bindiga – Gumi
Ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 1:00 na rana a unguwar Amazing Grace, Elepe da ke yankin Ikorodu.
Hundeyin, ya bayyana cewa sun samu kiran gaggawa daga yankin da ke nuna cewa an samu rikici tsakanin ma’auratan a cikin ɗakinsu.
A yayin rikicin, an ruwaito cewar mijin ya daɓa wa matar tasa wuƙa har lahira.
Daga bisani ya rufe ta a ɗaki, sannan ya ƙone ɗakin, daga bisani ya ji wa kansa rauni.
’Yan sanda sun isa wajen da lamarin ya faru, tare da kashe wutar, inda suka iske gawar matar kwance a ƙasa ɗauke da raunukan wuƙa.
An kai mijin asibiti domin a duba shi, daga baya kuma jami’an tsaro suka tsare shi.
Lokacin da ake masa, tambayoyi, wanda ake zargin ya amsa cewa ya daɓa wa matarsa wuƙa yayin da suka samu saɓani, kuma ya yi wa kansa rauni ne domin ɓatar da kama.
An ajiye gawar matar a asibitin Ikorodu, yayin da jami’an ke ci gaba da gudanar da bincike domin gano haƙiƙanin abin da ya faru.