Hukumar Yaki Da Yaduwar Cutar AIDS ta (ANASACA) ta Jihar Anambra, ta ce jihar ce ta biyar wajen yawan masu yada cutar a Najeriya.
Babban Daraktan (ANASACA) Johnbosco Ementa, ne ya bayyana hakan a taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya ranar Alhamis a Awka, babban birnin jihar.
- Charles III: Muhimman Bayanai Kan Sabon Sarkin Ingila
- NAJERIYA A YAU: Ruwa Ya Tashi Cinye Jihar Jigawa
Ya kuma ce cutar ta fi yaduwa ne a tsakanin matasa masu shekaru 15 zuwa magidanta masu shekaru 49.
Haka kuma a cewarsa, hukumar na aiki babu kakkautawa domin tabbatar da rage yaduwar cutar, ta hanyar wayar da kan al’umma game da dabarun hana yaduwarta.
“Muna aiki tukuru, tare da hada guiwa da sauran masu ruwa da tsaki don kawo karshen cutar AIDS a jihar.
“Haka kuma ina farin cikin sanar da ku cewa shirye-shirye sun yi nisa na fara aiwatar da sabuwar dokar hana nuna kyama ga masu dauke da cutar ta 2014 a Jihar Anambra.
A nasa bangaren, kwamishinan lafiya na jihar, Dokta Afam Obidike, ya koka kan yadda cutar ta AIDS take yaduwa babu kakkautawa, tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo karshenta.