Ana zargin wata matar aure mai suna Hajara Abubakar kan mutuwar kishiyarta mai suna Bilikisu Abubakar a kauyen Jiramo da ke Karamar Hukumar Takai a Jihar Kano.
Bayanai sun ce marigayiya Bilkisu Abubakar ta yanke jiki ne ta fadi daga bisani ta rasu jim kadan da yin hatsaniya da abokiyar zamanta Hajara Abubakar.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Haruna Abdullahi Kiyawa ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a ranar Larabar makon jiya da misalin karfe 10:00 na dare.
DSP Haruna ya ce Dagacin kauyen Jiramo Alhaji Ya’u Hamza ne ya sanar da ’yan sanda game da faruwar lamarin inda ya mika wadda ake zargin a hannunsu.
A cewar Kiyawa, “Wadda ake zargin ta yi fada da marigayiyar Bilkisu inda suka yi kokawa, a wannan lokaci ne kuma marigayiyar ta yanke jiki ta fadi kuma ta ce ga garinku nan. A yanzu haka wannan mata tana hannunmu a Sashen Binciken Manyan Laifuffuka don ci gaba da bincike. ”
DSP Haruna ya ce an ajiye gawar marigayiyar a Asibitin Kwararu na Murtala Mohammed.