✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin ’yan Najeriya da satar N720m a wurin aikinsu

Sallamar ’yan Najeriya daga kamfanin ya haddasa rikici tsakaninsa da kungiyar ma'aikatan jiragen saman Najeriya

An sallami wasu ’yan Najeriya bakwai daga aiki kan zargin satar Naira miliyan 720 (Dala 600,000) da kamfanin da jiragen sama na kasar Turkiyya da suke aiki ya yi musu.

Sallamar ’yan Najeriya daga kamfanin ya haddasa rikici tsakaninsa da kungiyar ma’aikatan jiragen saman Najeriya, lamarin da ya sa kamfanin zarge kungiyar da goyon bayan ma’aikatan nasa da yake zargin sun sace masa Dala dubu dari shida.

Kamfanin ya fitar da bayanin abin da yake zargi ne kwanaki kadan bayan kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta yi wata zanga-zangar lumana a kofar ofishinsa.

A cewa kamfanin, ma’aikatan sun yi wuru-wurun tikitin jirgi na Dala 600,000 a shekarar 2023, wanda hakan ya janyo masa gagarumar hasara.

Kungiyar NLC dai ta janye Zanga-zangar amma ta musanta zargin almundahanar.

Amma kamfanin ya ce ya gudanar da bincike mai zurfi kan lamarin tare da kungiyar ma’aikatan jirgin saman Najeriya, kuma sun tabbatar da faruwar lamarin.

A cewar kamfanin, bayan tabbatar da laifin maaikatan ne aka ba su damar rubuta takardar ajiye aiki da kansu.

A cewarsa, uku daga ciki sun rubuta hudu kuma suka ki, duk da cewa kafin kammala binciken duk wadanda ake zargin sun nemi a ba su dama su rubuta takardar ajiye aiki na kashin kai.

Sai dai shugaban kungiyar NLC a Legas, Kwamared Funmi Sessi ya shaida wa wakilinmu cewa zargin damfarar dala 600,000 ita ma damfara ce.