✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin wani matashi ya kashe wansa

Ana zargin wani matashi mai shekara 18 da kashe wansa saboda ya hana shi fada da wani. Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe…

Ana zargin wani matashi mai shekara 18 da kashe wansa saboda ya hana shi fada da wani.

Lamarin dai ya faru ne da misalin karfe 9.00 na daren Litinin a garin Zuba na Yankin Babban Birnin Tarayya.

Aminiya ta samu labarin cewa tun da farko, wanda ake zargin ya harzuka ne bayan da ya samu wasu masoya biyu, mace da namiji suna tadi ko zance a kofar gidansu.

Wani dan unguwar mai suna Abdullahi ya sanar da wakilinmu cewa yaron ya bukaci masoya biyun da su bar wajen, lamarin da ya koma husuma a tsakaninsu.

“Nan take ya shiga cikin gida ya fito da wuka”.

A cewar Abdullahi, wan matashin mai kimanin shekara 20 ya nufo wanda ake zargin a guje, bayan an ankarar da shi, “yana yunkurin hana shi yin fadan, sai ya juya ta kansa, ya caka masa wukar a wuya”.

Aminiya ta samu labarin cewa matsahin ya gudu bayan faruwar lamarin.

Tun a daren aka sanar da ‘yan sanda lamarin; bayan sun tantace gawar sun dauki hotonta kuma aka yi mata sutura.

Sai dai a cewar majiyar, ‘yan sandan sun sake komawa ranar Talata suka bukaci gawar, bayan an riga an yi mata sutura, suka wuce da ita zuwa Babban Asibitin Kubwa inda aka tabbatar da mutuwar.

Bayan nan ne aka yi wa marigayin sallar jana’iza aka binne shi.

Babban jami’in ‘yan sanda na Zuba, CSP Lamido Alkali, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ce matsahin da ake zargi ya gudu tun gabanin a sanar da su.