✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin tsohuwa mai shekara 107 da sa wa a kwakule idon yaro don ‘hada layar bata’

Sai dai tsohuwar ta musanta zargin, inda ta ce ita maganin gargajiya take bayarwa

Wani matashi a Kano ya shiga komar ’yan sanda bisa zarginsa da kwakule idanun wani yaro a unguwar Dantsinke da ke Karamar Hukumar Tarauni a Jihar Kano, din hada layar bata.

Ana dai zargin matashin mai kimanin shekara 17 da haihuwa Mai suna Isah Hassan wanda aka fi sani da Shahidai da kwakule idanun mai kimanin shekara 12 da haihuwa, mai suna Mustapha Yunusa, bisa umarnin wata tsohuwa.

Shahidai ya cire idanun Mustapha ne bisa umarnin wata tsohuwa mai maganin gargajiya mai suna Furera Abubakar mai kimanin shekara 107 da za ta hada masa layar bata.

Sai dai Sayyada Furera Abubakar ta musanta laifin da ake zarginta da shi inda ta ce ta yi kokarin taimakon yaron ne da maganin gargajiya.

“Ni mai maganin gargajiya ce karya yake min. Ina da jikoki sama da 50 ban kuma cire musu nasu idanun ba, me ya sa zan yi hakan ?”

Yayin da yake zantawa da manema labarai, mahaifin yaro Mustapha, Malam Dahiru Ahmad ya ce ya kai yaron wurin amininsa Malam Arma inda ya ke makaranta a unguwar ta Dantsinke.

“An kira ni cewa yarona yana Asibitin Kwararru na Murtala Mohammed ga kuma abin da ya faru da shi. Lokacin da na isa Asibitin sai ake gaya min cewa wasu bata gari sun sace shi tare da kai masa hari har sun kai ga cire masa idanu. To sai kuma a jiya na sake samun kira cewa an kama yaron da ya cire idanun dana har ma ya yi ikirarin cewa shi ya aikata laifin,” inji mahaifin yaron.

Malam Dahiru ya jinjina wa jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi tun daga farkon lamarin har zuwa kama wanda ake zargin.

Ali Abdulhamid jami’in tsaro ne nabijilanti a Dantsinke ya bayyana cewa sun kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake yunkurin cire wa wasu idanun.

“Mun kama Shahidai akan iyakar Kumbotso da Tarauni bayan ya cire idanun makonni biyu sai ga shi cikin ikon Allah mun kama shi a lokacin da yake kokarin cire wasu idanun. Wani daga cikin ma’aikatanmu ya gaya mana cewa wani ya nemi taimakonsa akan aikata wani laifi.

“Da muka ji irin laifin sai muka shirya masa yadda zai yi masa tarko. A lokacin ya nemi ya taho da wuka zuwa wurin da zai gudanar da laifin inda kuma a karshe muka yi nasarar kama shi,” inji shi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbattar da faruwar lamarin inda ya ce jami’ansu na gudanar da bincike, kuma da zarar sun kammala, za su gurfanar da shi a gaban kuliya.