’Yan sanda a yankin Hadeja da ke Jihar Jigawa sun kama tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kafin-Hausa Malam Aliyu Muhammad Kwatalo bisa zarginsa da daukar da wata matar aure mai suna Fatima Usman da nufin yin lalata da ita a wani gidansa da ke rukunin gidajen ma’aikatan Karamar Hukumar Hadeja (LGA Kuarters).
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Jigawa SP Audu Jinjiri wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce mijin matar ne ya kama wanda ake tuhumar saboda ya ji tana waya da wani inda shi kuma ya labe yana kallon lokacin da tsohon Ciyaman din ya zo ya dauki matar tasa a mota, inda ya bi su har zuwa inda ya shiga da ita wani gida daga nan ne ya sa kwado ya kulle kofar gidan ta baya, ya rika yin kururuwa ya tara jama’a a kofar gidan.
Ya ce wanda ake zargin ya tsallaka ta kan katanga ya tsere ita kuma matar a daidai lokacin da ta yi yunkurin hawa katanga don tsallakewa sai ta fado ba daidai ba har ta karye a kafa lamarin da ya sa jama’a suka kama ta suka mika wa ’yan sanda. Daga nan ne ’yan sanda suka kamo wanda ake zargin bayan sun tsananta bincike.
Wata majiya ta ce mijin matar ne ya shigar da korafi ga ’yan sanda a kan wanda ake zargin wanda hakan ya sa aka kamo shi a ranar Talatar makon jiya aka tsare su tare da matar zuwa ranar Laraba kafin a bayar da belinsu.
Kakakin ’Yan sandan ya ce yanzu haka wanda ake zargin yana amsa wasu tambayoyi kuma da zarar sun kammala bincike za su mika shi ga kotu don a zartar masa da hukuncin da ya dace da shi.
Bayanan da suke fitowa sun ce tsohon shugaban karamar hukumar yana ta kai-komo a tsakanin iyayen matar da mijinta don a sasanta batun kafin a kai ga zuwa kotu.
Wata majiya ta shaida wa wakilinmu cewa mijin Fatima ya nemi a biya shi wasu makudan kudi kafin ya janye karar don ya samu damar aurar wata mata, ita kuma wadda ake zargin ya amince ya sake ta.
Lokacin da wakilinmu ya tuntubi tsohon shugaban karamar hukumar don jin ta bakinsa a kan wannan zargi da ake yi masa, ya ce ba zai yi magana ba, inda ya shaida wa wakilinmu cewa ya je ya buga duk abin da ya ga dama, amma babu abin da zai iya cewa.