✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin malami da yi wa dalibarsa fyade a Jigawa

'Yan sanda na bincike kan lamarin don gano gaskiya.

‘Yan sanda a Jihar Jigawa na binciken wani malamin makaranta da ake zargin ya yi wa dalibarsa fyade.

Shekarar wanda ake zargin 30 da haihuwa, kuma ya fitone daga kauyen Shuwarin a Karamar Hukumar Kiyawa.

An zargi malamin, wanda ke koyarwa a Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Shuwarin, da laifin lalata da dalibarsa mai shekara 19 a bandakin makarantar.

  1. An dawo da sharan karshen wata a Gombe
  2. Yawan mutanen da COVID-19 ta kashe a Indiya sun haura 400,000

Kakakin ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shisu Adam, ya tabbatar da fara bincike a kan lamarin a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.

Kazalika, ya tabbatar a cewa idan aka samu wanda ake zargi da laifi za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Jigawa na cikin jihohin arewacin Najeriya da suka kafa dokar hukunta masu aikata fyade.

A watan Fabrairun da ya wuce ne gwamnan jihar, Muhammadu Badaru Abubakar, ya sanya hannu a kan dokar, kuma Majalisar Jihar ta amince da ita.

A karkashin sabuwar dokar da gwamnatin jihar ta kafa, za a yanke hukuncin kisa a kan duk wanda aka samu da laifin aikata fyade.