Wani malamin makaranta a garin Asaba na Jihar Delta, ya shiga hannun jami’an ’yan sanda saboda zarginsa da yi wa wani yaro mai wata 19 a duniya bulala 31, wadda ta yi sanadin ajalinsa.
Rotanni sun ce yaron ya yi dogon suma ne bayan malamin nasa ya yi masa tatas da bulala saboda wani laifin da ya masa a ranar Litinin din da ta gabata.
Tuni dai Gwamnatin Jihar ta rufe wata makarantar firamaren da lamarin ya faru a garin Asaba sakamakon mutuwar dalibin.
An gano cewa yaron ya mutu ne sakamakon raunin da ya samu bayan bugun da malamin nasu mai suna Emeka Nwogbo ya yi masa.
An ce yaron ya yi rashin lafiya bayan dukan, kuma an kai shi Babban Asibitin Tarayya da ke Asaba, wanda daga bisani ya ce ga garinku nan a ranar Asabar.
Kwamishinan Ilimin Jihar, Chika Ossai, ya shaida cewa tun farko ma makarantar ba ta samu amincewar gwamnatin Jihar ba.
Ya kara da cewa gwamnati ta yanke shawarar rufe makarantar ne saboda mai makarantar ba shi da lasisin aiki.
A halin da ake ciki, malamin da ake zargi yana hannun ‘yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar, DSP Bright Edafe, ya ce suna kan gudanar da bincike kan mutuwar yaron.