✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin mahaifi da kashe dansa da tabarya a Kano

Ana zargin mahaifin ne da yin amfani da tabarya wajen hallaka dan sa mai shekara 10.

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta kama wani mahaifi mai suna Malam Lawan Bello da ke Unguwar Kurna a Karamar Hukumar Dala a jihar bisa zarginsa da kisan dansa.

Rahotanni sun ce wanda ake zargin ya yi amfani da tabarya ce wajen hallaka dan sa mai shekara 10 da haihuwa.

Wata majiya ta kishiyar uwar yaron ce ta yi karar dan ga mahaifinsa cewa idan ta aike shi yana dadewa, hakan ya sa uban ya rufe dan a daki ya rika dukansa da tabarya sai da ya daina numfashi.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da kama Lawan bayan da ya yi yunkurin tserewa. Ya ce “Bayan samun wannan rahoto Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Kano, Mista Sama’ila Dikko ya tura ’yan sandan inda suka je gidan da gagagwa suka dauki yaron suka kai shi Babban Asibitin Murtala Mohammed inda likita ya tabbatar da rasuwarsa.”

DSP Kiyawa ya kara da cewa, “Yanzu haka wanda ake zargi yana hannunmu inda ya tababtar da cewa shi ya kashe yaron da hannunsa a dalilin wai yaron ba ya jin magana. Har ila yau kuma ana ci gaba da fadada bincike da zarar an kamamla za a gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu don hukunta shi.”