✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana zargin basarake da yi wa yaro fyade a Zariya

’Yan Sanda sun cafke wani basarake a Masarautar Zazzau bisa zargin sa da yi wa wani yaro mai shekara 14 fyade

’Yan Sanda sun cafke wani basarake a Masarautar Zazzau bisa zargin sa da yi wa wani yaro mai shekara 14 fyade.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige, ya tabbatar da cafke basaraken a zantawarsa da manema labarai a Zariya.

Jalige ya ce ’yan sanda na ci gaba da binciken lamarin kuma da zarar sun kammala bincikensu za su gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.

Mazauna anguwar Kwarbai da ke cikin birinin Zariya sun bayyana cewa sun shekara kusan 20 suna zargin basaraken da yi wa kananan yara maza fyade.

Dan uwan yaron da aka yi wa fyaden, ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya faru ne a gidan basaraken da ke unguwar Kwarbai.

Ya kara da cewa, “yaron makwabcin basaraken ne, kuma yana daukar sa a matsayin uba.

“Sai basaraken ya aike shi dakinsa ya dauko masa kudi, a yayin da taron ya shiga daki ne sai ya biyo shi a baya ya rufe kofa ya dauki wuka ya ce zai kashe shi idan ya yi ihu, daga bisani ya aikata mummunan aikin ga yaron.”

Ya ci gaba da cewa, “yaron ya dimauce bisa abin da ya faru da shi wana ya kasa sanar da mu, sai ya je ya sanar da kanwar mahaifiyarsa inda ita kuma ta sanar da mu.

“Jin haka ya sa muka tara yan uwa don daukar matakin kai kara ofishin yanki na ’yan sanda na cikin birnin Zariya.”

Wakilin Aminiya ya garzaya Sashen Kula Da Cin Zarafin Mata da Yara na Asibitin Gambo Sawaba da ke Kofar Gayan a Zariya, inda aka yi gwaje-gwajen.

Shugabar Sashen, Hajiya Aishatu Ahmed, ta tabbatar da cewa “’yan sanda da ke Fada, Zariya sun kawo yaron don a duba lafiyarsa, tare da wanda ake zargin ya aikata fyaden kuma mun bai wa ’yan sanda sakamakon bincikemmu.”