✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin Bagudu da boye Kudaden Abacha

Bagudu na hannun daman Buhari ne kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin APC.

Ana zargin Gwamnan Jihar Kebbi, Abubakar Atiku Bagudu, da boye kudaden da ake zargin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Sani Abacha, ya wawure.

Wani binciken kwakwaf da ’yan jarida 600 daga kasashe 150 suka dauki tsawon lokaci suna gudanarwa da sunan ‘Pandora Papers’, ya ce ya gano wani lokaci da gwamnan Kebbin ya tura wata tawaga zuwa kasar Singapore ta nemo wata sabuwar maboya mai wuyar ganowa domin kai kudaden na Abacha.

Ana zargin kudaden na daga cikin biliyoyin dalolin da ake zargin Atiku Bagudu ya taimaka wa iyalan marigayi Abacha karkatarwa a shekarun 1990, wadadndan da halin yanzu ake tafka shari’a a kasar Amurka domin a kwace su.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin gwamnan wanda ya musanta zargin da aka masa, amma abin ya faskawara; Sai dai lauyansa, ya ce duk abin da yake yi yana yin sa ne cikin ka’ida tare da kiyaye doka.

– Na hannun dama Buhari

Atiku Bagudu dai shi ne Shguaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar APC mai mulki kuma babban na hannun daman Shugaban Kasa Muhamamdu Bauhari ne.

Wasu majiyoyi sun ce saboda matsayinsa a kungiyar gwamnonin APC da kuma kusancinsa da Buhari, shi da Shguban Rikon Jam’iyyar APC na Kasa kuma Gwamnan Yobe, Mai Mala Buni, ne masu wuka da nama wajen zaba wa Buhari wanda zai gaje shi idan ya sauka daga mulki, da ma wanda zai zama shugaban jam’iyyar na kasa.

  1. – Buhari na fuskantar matsin lamba

A halin yanzu dai Shugaba Buhari na fuskatar matsin lamba cewa lallai ya binciki makusancin nasa tare da sauran manyan ’yan Najeriya da binciken ‘Pandora Papers’ yake zargi da aikata nau’ika daban-daban na almundahanar kudade da mallakar kadarori a kasashen waje ta haramtacciyar hanya.

Kungoyi da daidaikun mutane na matsa shugaban kasar lamba cewa ya umarci hukumomin da suka dace su binciki mutanen da ake zargin, kamar yadda gwamnatinsa take bugun kirji da yaki da rashawa.

  1. – Binciken ‘Pandora Paper’

Binciken ‘Pandora Papers’ dai ya mayar da hankali ne wajen gano yadda ’yan siyasa da attajirai da masu fada a ji a kasashen suke azurta kawunansu ta kazamar hanya.

’Yan jaridar da suka gaudanar da binciken sun farauto muhimman bayanan huldodin kudade da takardun gwamnati sama da miliyan 11.9, tare da bin diddiginsu domin gano irin badakalar da ke kunshe a ciki ma’amalolin.

Yanzu dai idanu na kan Buhari don ganin matakin da zai dauka kan ’yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da attajiran da sauran ’yan Najeriya wandadan binciken ‘Pandora Papers’ ya fallasa, ciki har da Bagudu.

Daga cikin ’yan ’yan siyasa da manyan jami’an gwamnati da attajirai da masu fada a ji a Najeriya da aka gano a cikin binciken har da wani tsohon Babban Alkalin Kasar da ’yan majalisar dokoki da wani babban fasto.

Sauran sun hada da tsohuwar Ministar Albarkatun Man Fetur, Stella Oduah da tsohon Gwamnan Jihar Anambra kuma tsohon dan takarar Mataimakin Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben 2021, Peter Obi.