Mazauna yankin Kofar mata a birnin Kano na zanga-zanga bayan kashe wani matashi da jami’an ’yan sanda suka yi ranar Lahadi.
Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta ce mamacin mai suna Saifullahi, wanda ya gamu da ajalinsa ne a hannun ’yan sanda, biyo bayan sun azabtar da shi.
- Yadda aka tarwatsa zanga-zangar #EndSARS a ofishin CBN
- Kasafin 2021: Noma da Arewa maso Gabas na bukatar kudade —Monguno
- An kaddamar da shirin tallafin N75bn domin matasa
’Yan sanda sun kama Saifullahi mai shekaru 17 ne a lokacin da suka kai sumamen kama wasu bata-gari.
Sai dai zanga-zangar ta soma ne yayin da jami’an ’yan sanda suka kai gawar matashin gidansu a safiyar Litinin.
Hakan ya sa wasu fusatattun matasa suka dauko gawar mamacin suka ajiye ta a bakin ofishin ’yan sandan da ke yankin Dan Dawaki, kuma suka tare titin Kofar Mata tare da kona tayoyi suna rera wakokin neman kawo karshen zaluncin ’yan sanda domin nuna fushinsu dangane da abin da ’yan sandan suka aikata.
Kakakin Rundunar ’Yan Sanda na Jihar Kano, Abdullahi Haruna Kiyawa, ba daga wayarsa ba a lokacin da aka nemi jin ta bakinsa.
Idan ba a manta ba, tsawon kwanakin 12 ke nan matasa a Najeriya ke gudanar da zanga-zangar neman Gwamnatin Tarayya ta kawo karshen zaluncin ’yan sanda a fadin kasar.