A halin yanzu babu kwanciyar hankali yayin da ake shirin soma zabe a Unguwar Gawuna da ke Karamar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano.
A nan ne dai ake sa ran dan takarar Gwamna na jam’iyyar APC kuma Mataimakin Gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna zai kada kuri’arsa.
- An kama matashi da makamai a Kano
- Rikici ya barke a mazabar Abba Gida-Gida da Abdullahi Abbas a Kano
Sai dai gabanin tabbatuwar hakan, har jami’an ’yan sanda da aka baza a yankin domin shirin ko ta kwana sun bukaci karin ma’aikata, la’akari da yadda rikici zai iya fantsama a kowane lokaci.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, ’yan daba da suka yi lamo a yankin sun shiga taitayinsu yayin da jami’an Hukumar DSS suka hallara a wurin.
Amma dai bayan barin jami’an na DSS, yanayi na firgici ya sake mamaye yankin.
Jihar Kano dai na daya daga cikin Jihohin da tun kafin yanzu an yi hasashen za a yi gumurzu saboda tsananin adawa ta siyasa da ke tsakanin jam’iyyar NNPP da kuma mai mulki ta APC.