Wani mutun mazaunin kauyan Dilake da ke cikin karamar Hukumar Dutse, Jihar Jigawa ya yi karar wasu mutane uku da yake zargin sun yi wa ’yarsa cikin shege. Mutanen sun hada da Safiyanu Nasiru da Ibrahim Barau da kuma Abba Haruna, wadanda dukkansu ma’aikata ne a cikin garin Dutse, kamar yadda kotu ta shaida wa wakilinmu.
Mutumin mai suna Ali Abdullahi Dilake, ya yi karar mutanen nan da farko a gaban ’yan sanda kafin daga bisani su kuma suka gabatar da su a gaban kotu. Ya yi karar ce sakamakon bayanan da ’yarsa mai suna Aminatu Aliyu ta yi masa, cewa wadancan mutane ne suka yi mata cikin. Ya ce diyarsa tana da cikin wata biyar a jikinta.
A lokacin da dan sanda mai gabatar da kara yake wa alkali jawabi, ya ce ’yan sanda sun gabatar da Safiyanu Nasiru da Ibrahim Barau a gaban kotu amma Abba Haruna ya gudu, amma suna kan nemansa ruwa a jallo.
Kamar yadda yarinyar ta shaida wa ’yan sanda, cewa ta yi dukkansu sun yi lalata da ita a wurare daban-daban, ba ta san iyaka ba, bullar cikin a jikinta fili ne ya sa iyayenta suka ankara, hankalinsu ya tashi, sannan ta bayyana masu wadanda suka yi mata cikin.
daya daga cikin wadanda ake zargin dai ya musanta aikata laifin. A yayin da shi kuwa Ibrahim Barau ya amsa laifin, sai dai kuma ya roki alkali da ya yi masa sassauci a yayin yanke masa hukunci.
Alkalin kotun dai ya dage shari’ar zuwa kwana 14 masu zuwa.
Ana tuhumar mutum 4 da yi wa budurwa ciki a Jigawa
Wani mutun mazaunin kauyan Dilake da ke cikin karamar Hukumar Dutse, Jihar Jigawa ya yi karar wasu mutane uku da yake zargin sun yi wa…