✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana takun-saka tsakanin hukuma da ’yan Tijjaniyya kan hana Wazifa a makarantun Tsangaya

Hana Wazifa a makarantun Tsangaya a Jihar Bauchi da Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar (SUBEB) ta yi ya jawo cece-kuce a tsakaninta da ’yan darikar…

Hana Wazifa a makarantun Tsangaya a Jihar Bauchi da Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar (SUBEB) ta yi ya jawo cece-kuce a tsakaninta da ’yan darikar Tijjaniyya a jihar.

Wani malamin Musulunci Dokta Fatihi dahiru Usman Bauchi ya yi zargin cewa, tun zuwan gwamnatin jihar suka fara ganin abubuwan da suka fara ta da musu da hankali, inda ake kokarin tattake su ta kowace fuska a mayar da su ’yan Izala da karfi da ya ji su da ’ya’yanmu. 

Ya ce akwai abubuwa da yawa da gwamnatin ta yi da suka dauka neman tsokana ne ko ta da hankali  a Hukumar SUBEB a karkashin jagorancin Farfesa Ibrahim Yahaya Yero. 

Ya ce “Na farko ya kafa kwamiti wai zai sake manhajar makarantun Islamiyya amma a rediyo muka ji kuma duk wadanda ya sa a kwamitin ’yan Izala ne. Ya ce wai wani kwamiti ne da Izala ta kafa ya ba da wannan manhaja ya ce a duba a sanya shi a makarantun Islamiyya. Sai muka hadu dukan kungiyoyin da suke da makarantun Islamiyya a Bauchi muka yi wani kwamiti mai karfi muka ce uwar kungiyoyin makarantun Islamiyya ita ce Riyala ita ma ta kai kokenta ga hukumar amma ba a ce musu komai ba, da muka yi wannan kwamiti sai muka rubuta takarda ga Gwamnatin Jihar Bauchi cewa ba mu yarda ba a ce SUBEB ne za su yi mana manhaja don mun san shugaban dan Izala ne, wadanda ya sa a kwamitin dukansu ’yan Izala ne akidar Izala kuma Wahabiyanci ne mu muna bin Mazhabar Malikiyya ne. Har yanzu muna bin sawu don a yi gyara a sanya mutanen kirki a cikin kwamitin ko a rusa kwamitin gaba daya domin ko sun yi ba za mu yi amfani da manhajar Izala ba.”

Ya ce na biyu akwai makarantun Tsangaya da gwamnatin baya ta bude 100 a kasar nan kowace jiha an gina uku, a Jihar Bauchi ma an gina daya a Bauchi, daya a Sade daya a Azare. Ya ce, “Lokacin da tsohon Mataimakin Shugaba kasa Namadi Sambo ya zo ya bude wata makarantar Maulana Sheikh dahiru Bauchi ya ce za su gina makarantu 100 kai ma ka sama mana fili zan sa a gina maka Makaranta daya taka. Sai Shehu dahiru ya samar da fili Gwamnatin Tarayya ta gina kusan it ace ta karshe daga cikin wadanda aka gina aka bude makarantar gwamnati na tallafa wa daliban da abinci suna biyan wadansu daga cikin malamai Sheikh yana taimaka wa wadansu daga cikin malaman. Idan an zo daukar dalibai sai a yi raba-daidai, Sheikh ya kawo yara 50 daga cikin gari a kawo yara 50. Da wannan gwamnati ta zo sai SUBEB ta ce ta soke wannan tana kokarin kwace makarantar gaba daya, ta kori shugaban makarantar ta soke daukar daliban sakandare sannan ta dauki dalibai 100 da kyar ta bai wa Shehi mutum takwas alfarma, kuma abin mamaki da neman tsokana sai motar Izala ta wa’azi dauke da tambarin Izala ta dauko dalibai tana kawo su makarantar don Allah wannan ba tsokana ba ne?”

Ya ce na uku, sai hukumar ta SUBEB ta aiko da takardar hana Wazifa da karanta Salatul Fatihi a makarantar wanda yin hakan neman ta da hankali da fitina ne, a baya ma ya hana yin maulidin Manzon Allah (SAW).

Dokta Fatihi ya ce wadannan abubuwa ne suka tayar musu da hankali suke neman a yi musu adalci a yi gyara domin darikar Tijjaniyya wanda ya ga dama yake so ne yake yi ba dole ba ce, idan kuwa akwai ’yancin yin addini kowa na da iko ya yi addinin da yake so.

Da Sheikh dahiru Usman Bauchi ke mai da martani kan hana yin Wazifa da Maulidi da karanta Salatil Fatihi a makarantun Tsangayar, ya ce “Mu ’yan Tijjaniyya a Najeriya muna son mu aika wa dukan gwamnatoci tun daga kan Shugaban kasa da sauran masu rike da madafun iko cewa, da ake cewa kowa na da ’yancin yin addinisa shin ban da ’yan Tijjaniyya ne a cikin wannan doka ta kasa? Me ya sa ake tsananta wa ’yan Tijjaniyya a makarantun gwamnati?”

Malamin ya ce “Muna fara shaida wa Antoni Janar da dukan wanda harkar shari’a da kotuna suka shafa a duba mana wannan abu ya yi kusa ya tayar mana da hankalin kasa baki daya.” 

Ya ce duk makarantun gwamnati a Najeriya ’yan Izala suna hana a yi Wazifa da taron Maulidi da karanta Salatul Fatihi, alhali makarantun ba nasu ba ne na gwamnati ne. “Saboda haka muna kira a janye wannan ka’ida da za a matsawa ’yan Tijjaniyya a hana su ’yancin yin addininsu a makarantu,” inji shi.

Ya ce, suna bukatar a kawo dokar Najeriya da ta hana yin Wazifa ko ta hana karatun Salatul Fatihi a Najeriya a ga lamba ta nawa ce, kuma a wace shekara aka kafa dokar. “Kawai don muna da kunya muna da mutunci mun yi shiru sai a mai da kasarmu kasar Izala, wallahi ba za mu yarda ba,” inji Shehin.

Ya ce duk wanda aka hana shi Wazifa ko yin Maulidi ko Karanta Salatul Fatihi ya kai kotu, ya ji dalili. 

Shehin ya ce “Ko gwamnatin soja ce ta yi mana haka ba za mu yarda ba balle gwamnatin farar hula, ba a gwamnati sai da mutane, kuma alhamdulillahi muke da mutane wadanda duniya take kallonsu da addini da mutunci. A cikinmu ne fa ake samun Sherif Ibrahim Saleh wanda shi abin nunawa a duk duniya ma gaba daya balle Najeriya, bayan sanin Alkura’ni da Hadisi da sanin ruwaya da sauran fannonin ilimi addini kuma shi Sharifi ne  ta wajen mahaifinsa Sharifi ne Husainiyyi, mahaifiyarsa ma Sharifiya ce Hasaniyya, abin nunawa ne a duniya gaba daya kuma yana tare da mu.”

A zantawarsa da manema labarai Shugaban Hukumar SUBEB ta Jihar Bauchi, Farfesa Yahaya Ibrahim Yero ya ce babu gaskiya a cikin zargin zai mayar da kowane dan makarantar Tsangaya dan Izala. Ya ce sun aike da sako ga kowane shugaban makarantar Tsangaya ce bayan samun korafe-korafen da hukumarsa ta yi daga jama’a da iyayen yara kan batun. Ya ce, “Wadansu iyaye sun kawo mana korafin cewa ana tilasta wa ’ya’yansu yin Wazifa da Salatul Fatihi duk bayan Sallar Magriba da Isha, kuma hakan bai daga cikin tsarin koyawar marakarantun Tsangayar.”  

 Sugaban ya ce “Kowane dan kasa yana da ikon ya yi addininsa yadda ya fahimta ba tare da an tauye masa hakki ba, don haka ba mu hana kowa yin addininsa ba; maganar wai ni da ma’aikatana muna kokarin tilasta kowane dan makarantar Tsangaya ya su zama dan Izala ba gaskiya ba ce.”    

FarfesaYero ya ce “Don haka ne muka ce duk wani abin da bai daga cikin manhajar kowaya a makarantun Tsangayaa bari, mun tsaya kai da fata ba za mu taba bayar da kofar shigo da wani abu ba, don haka muna sanar da cewa muna da takardun da Hukumar UBEC ta shimfida kan manhajar koyarwarwa a makaratun Tsangaya.”  

 Dangane da wasikar da suka aike wa makarantun Tsangayar a jihar, Yero ya ce suna nan a kan bakarsu ba za su taba bari a shigo da abubuwan da ba su cikin mahanjar koyarwa ta Tsangaya a jihar ta Bauchi ba.