A kasar Syria, an shiga kwana na uku ana gwabza kazamin fada tsakanin mayakan kungiyar ISIS da na Kurdawa, inda akalla mutum 70 aka kashe ya zuwa yanzu.
Fadan dai ya faro ne bayan wani hari da dakarun ISIS din suka kai wani gidan yarin da ke kunshe da mambobinsu a ciki.
- An tsare shanu 44 a Bayelsa saboda karya dokar hana kiwo ta Jihar
- Matasa na zanga-zanga a Gashuwa bayan soja ya bindige direba
Harin, wanda aka kai gidan yarin Ghwayran, shi ne irinsa mafi muni da kungiyar ta kai tun bayan da aka ayyana yin galaba a kanta, kimanin shekara uku da suka wuce.
“Akalla dai mayakan Kurdawa 28 da wasu fararen hula biyar da kuma mayakan ISIS 45 ne aka hallaka,” inji Rami Abdel Rahman, Shugaban wata cibiya ta Birtaniya da ke sa ido kan kare hakkin dan Adam a Syria.
ISIS dai ta kaddamar da harin ne ranar Alhamis a kan gidan yarin da ke kunshe da fursunoni kusan 3,500, wadanda ake zarginsu da kasancewa ’yan kungiyar.
Maharan dai sun kwace makaman da suka samu a kukukun, sannan suka saki fursunoni da dama.
An dai sake kama daruruwan fursunonin daga bisani, amma har yanzu akwai wadanda suka cika wandonsu da iska.
Mayakan Kurdawan dai tare da goyon bayan jiragen yakin Amurka na can sun yi wa kurkukun kawanya, a kokarinsu na sake kwace iko da shi.