’Yan Arewa mazauna yankunan Karamar Hukumar Mbano a Jihar Imo da aka fi kai musu hare-hare ana yi musu kisan mummuke, sun ce, ’yan awaren Biyafara sun ce za su ci gaba da kashe su matukar Gwamnatin Tarayya ba ta sako jagoransu Nnamdi Kanu ba da take tsare da shi ba.
’Yan awaren Biyafara IPOB suna zafafa hare-hare a ofisoshin ’yan sanda a sassan jihar da kuma kai wa ’yan Arewa da ba su ji ba, ba su gani ba mazauna kauyuka hari.
- Dalibar da aka yi wa sharrin safarar kwayoyi zuwa Saudiyya ta zama jami’ar NDLEA
- Mata ta kwara wa mijinta acid bayan takaddama a tsakaninsu
A makon jiya ’yan IPOB sun kashe ’yan Arewa mazauna Jihar Imo su 10, yayin da a kauyen Anayara kuma suka kai wa wadansu ’yan kasuwa hari suka harbi mutum biyu, daya a hannu daya kuma a ciki haka siddan.
Salisu Abdullahi da aka harba a ciki ya shaida wa Aminiya cewa, “Abin da ya faru gare ni, wadansu ne suka zo suka harbe ni, ina sayar da nama a garin Anayara, sun harbe ni a hannu, sun harbe ni a kirji sannan a ciki.”
A halin yanzu likitoci sun samu nasarar yi wa Salisu aiki yana kwance a wani asibiti a garin Okigwe.
Ya ci gaba da cewa, mutum uku ’yan awaren Biyafara ne suka zo a cikin mota suna fitowa suka bude musu wuta.
Har ila yau ya ce sai da aka ajiye wa likitoci Naira dubu 114, kafin a yi masa aiki.
“Eh, gaskiya ne sun ce haka nan sojojin da suka kawo mu asibitin ne suka rattaba hannu suka fara yi min aiki.
“Duk kokarin da suke yi na sanar wa shugabannin ’yan Arewa babu wani mataki da suke dauka bare ya yi tasiri.”
Ta fuskar sanar wa jami’an tsaro kuwa ya ce, a duk yankin babu wani ofishin ’yan sanda saboda harin da suke kai musu babu ’yan sanda a wurin.
Shi kuma Basiru Muntari da aka harba a hannu lokacin da maharan suka je inda suke kasuwancinsu suka bude musu wuta, ya ce bayan an harbe shi a hannu sai ya yi kwance a karkashin tebur ya dora hannunsa a kirjinsa jini na zuba a rigarsa suna zaton ya mutu.
Ya shaida wa wakilinmu cewa, “Muna tsaye ne muna sayar da tsire ba zato ba tsammani, kawai sai muka ga mutane sun bude mota sun fito ba wani bayani suka bude mana wuta, suna ta harbin mu suka kashe mana mutum daya, daya yana asibiti ma yanzu haka, ni kadai ne Allah Ya tsare.
Sun harbe ni a hannu, su a tsammaninsu ma na mutu, saboda harbin da suka yi min bai same ni a zuciyata ba, harsashin a hannu ya same ni a tsakiyar hannu,” inji shi.
Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Imo, CSP Macheal Attam, dangane da inda aka kwana game da harin, sai ya ce, “Mun samu labarin sai dai muna bincike a kai, amma ba a kama kowa ba.