Fitaccen malamin addinin Islama a Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta yi duk mai yiwuwa wajen kawo karshen ayyukan ’yan bindigar da suka addabi kasar.
Sheikh Dahiru Bauchi ya kuma bayyana wajibcin gwamnati ta fitar da ’yan Najeriya daga halin tsoron da suke ciki, a lokacin da yake jawabi a majalisinsa, inda ya bayyana takaicinsa kan halin rashin tsaron da Najeriya ke ciki.
- Majalisa ta amince wa Buhari ya ciyo sabon bashin $5.8bn
- Yadda masu yi wa kasa hidima 5 suka rasu a hatsarin mota
Ya bayyana cewa, “Ba mu zabe su don mu zama haka ba, ba mu zabe su don mu zama abin tausayi irin wannan ba, ya zama ana kashe mu ba mai kariya ana sayar da mu kamar dabbobi — ana yin abin da aka ga dama da mu — alhali muna da gwamnatoci har guda uku a kanmu; Wannan abin kunya ne, abin dariya ne, abin kuka ne.”
Jawabin shehin malamin na zuwa ne kwanaki kadan bayan kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa sama da mutun 30 a Sabon Birni a Jihar Sakkwato, wanda ya haifar da zanga-zanga a Arewacin Najeriya.
’Yan bindiga sun dauki tsawon lokaci suna kashe-kashe da garkuwa da mutane domin karbar kudaden fansa, gami da yi wa mata fyade da kona garuruwa da dukiyoyi da sauran na’uikan ta’addanci, musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce, “Abin da yake wajibi ga gwamnatoci [shi ne] su kula su fitar da mu daga abin da muke ciki na tsoro —kana gidanka kana jin tsoro, kana waje kana jin tsoro, kana tafiya kana jin tsoro, alhali akwai gwamnatoci har guda uku a kanka.”
Ya yaddada kira ga Gwamnatin Tarayya da jihohi da kananan hukumomi su tashi tsaye domin yin duk abin da ya dace wajen samar da tsaro da kuma sauke duk nauyin da kundin tsarin mulki ya rataya a wuyansu na kare rayuka da dukiyoyi da kuma jin dadin al’ummar kasa.
“Duk muna daura muku nauyi na kuwala da rayukan jama’ar Najeriya da zaman lafiyar Najeriya da walwalar Najeriya; Ina aka ce kasa ko noma ba za a yi ba, to me za a ci?”