✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana gallaza wa dalibai Musulmai a jami’o’i mallakin Kiristoci a Najeriya – MURIC

MURIC ta kuma yi zargin ana tilasta wa Musulmai zuwa Coci a makarantun

Kungiyar Kare Muradun Musulmai a Najeriya (MURIC) ta yi zargin ana gallaza wa dalibai Musulman da ke karatu a jami’o’i musu zaman kansu mallakin Kiristoci a kasar nan.

Kungiyar ta fadi hakan ne a cikin wata sanarwa wacce Shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya sa wa hannu, ta kuma fitar a ranar Alhamis.

A cikin sanarwar, MURIC ta zargi jami’o’in da nuna gaba da tsana da kuma tsangwama ga Musulmi da kuma adddinin Musulunci ta hanyar yadda ake tirsasa dalibai Musulmai zuwa Coci da kuma hana su sa hijabi da sauransu.

“Mun samu rahotanni da yawa kan yadda jami’oin masu zaman kansu mallakin Kiristoci ke nuna wa dalibai Musulmai kyama da kuma wariya, ta yadda ba sa iya yin addininsu yadda ya kamata.

“Sannan kuma ba a barin su su kafa tare da gudanar da kungiyarsu ta dalibai mai alaka da addinin Musulunci…., mafi muni ga wannan shi ne rashin ba su inda za su yi ibadarsu ta Sallah,

“Haka kuma ana tilasta musu zuwa Coci yin ibada, a inda ake daukar sunaye, wadanda duk ba su halarta ba, kuma a hukunta su,” a cewar MURIC a cikin sanarwar.

Shugaban na MURIC ya ce hakan take hakkin dalibai Musulmi ne da Kundin Tsarin Mulkin kasar nan ya ba su, ya kuma yi kira ga hukumar kula da jami’oi ta kasa da ta gaggauta tsaftace wadannan jami’o’in.