✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana fama da karancin kwaroron roba a Kenya

Ma'aikatar Lafiyar Kasar ta ce gwamnati za ta yi kokarin magance matsalar.

Fatarar kwororon roba da ake fama da ita ta sanya gwamnati ta bukaci al’umma da su yi amfani da wasu dabarun cike gibin wannan kalubale a kasar Kenya.

Wani rahoto da BBC ya wallafa ya bayyana cewa kasar na fama da karancin kwaroron roba, inda alkaluma suka nuna cewa kwaroron robar miliyan 1.6 gwamnati ta samar madadin miliyan 455 da ya kamata a samar a shekara.

Jaridar Star Kenya ta ce wani rahoto da Asusun Yaki da Cutar Kanjamau da Tarin Fuka da Zazzabin Cizon Sauro, ya nuna cewa kwaroron roba miliyan 20 aka raba a kasar.

Sai dai jaridar ta kuma ambato Ma’aikatar Lafiyar Kasar tana cewa gwamnati za ta yi kokarin magance matsalar karancin kwaroron robar da ake fama da ita a kasar da ke Gabashin nahiyyar Afirka.

Bayanai sun ce wannan lamari ya haifar da muhawara musamman a kafafen sadarwa na Intanet, saboda yadda wasu ke la’akari da amfani da kwaroron robar domin kare yaduwar cututtuka da ake dauka ta hanyar jima’i da kuma hana daukar ciki.

Wasu rahotanni sun nuna cewa ana fuskantar matsalar karancin kwararon robar ce sakamakon haraji da gwamnati ta sanya wa kayayyaki.