✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ana fakewa da sunan rikicin Makiyaya don a raba kan Arewa’

Dole ne mu so juna, don mutumin Kudu bai san wata kabila Hausa Fulani ba, a ganinsa duk a dunkule muke.

Tsohon Gwamnan Jihar Nassarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ce ana fakewa da sunan rikicin makiyaya domin a raba kan al’umma a kasar nan.

Sanata Abdullahi wanda ke zaman dan Majalisar Dattawa mai wakiltar shiyyar Nassarawa ta Yamma, ya bayyana hakan ne yayin wata hirarsa da BBC, inda ya ce ana kokarin raba kan Hausawa da Fulani da sunan rikicin makiyaya da manoma a Arewacin Najeriya.

A hirar tasa, ya ce ana fakewa ne da sunan hare-haren da ake zargi makiyaya na kai wa wasu jihohin kasar da manufar raba kan al’ummar yankin.

A cewarsa, rikicin makiyaya ya samo asali ne sakamakon cinye hanyoyi da burtalai da sauran dazukan da aka kebe musamman domin makiyaya, sannan an gaza sama da wani tsari da zai ba su damar ci gaba da gudanar da harkokinsu.

“Ana neman dalili ne domin bata sunan makiyaya don a la’ance su, idan aka zo maganar kiwo wa yake wani batun Kudu? Sanin kowa ne cewa kiwo a Arewa yake, saboda haka wuta ce ake kunnowa don ganin ana raba kan al’ummar Arewa,” in ji shi.

Sanatan ya ce akwai bukatar gwamnati ta kawo karshen wannan matsala ta hanyar fahimtar barazanar da ke tattare da yadda ake kiwo barkatai ba tare da wani kyakkyawan tanadi ba.

Ya ce ya kamata gwamnati ta samar wa makiyaya wata hana da za su rika gudanar da harkokinsu ba tare da sun shiga hakki ko ketare iyakar al’umma ba.

“Dole ne mu so juna, don mutumin Kudu bai san wata kabila Hausa Fulani ba, a ganinsa duk a dunkule muke, saboda haka yanzu kuma so ake a raba kan Hausawa da Fulani,” a cewarsa.