✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ana fakewa da barace-barace wajen aikata miyagun laifuka —Hisbah

Wasu na basaja da barace-barace wajen aikata munanan dabi’u kamar karuwanci da sace-sacen waya.

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce, ta fara dakile barace-barace a kan tituna a jihar, lamarin da ya kai ga kama wasu mabarata kimanin 931 cikin makonni biyu.

Hisbah ta kuma koka da yadda ake amfani da wasu mabarata a matsayin ’yan leken asiri da debo wa wasu bata gari labarai, wanda hakan ke kawo barazana ga tsaro a jihar.

Babban Kwamandan Hukumar, Muhammad Haruna Ibn Sina ne ya bayyana haka a Kano, yayin da yake zantawa da manema labarai game da ayyukansu.

Ya ce, ana zargin akwai wasu daga cikin wadanda amfani basaja da barace-barace wajen aikata wasu munanan dabi’u a zamantakewa.

Ya ce, “A kokarinmu na tsaftace Kano ta hanyar haramta barace-barace, Hukumar Hisbah ta kama mabarata kimanin 931 a cikin makonni biyu kacal.

Wasu daga cikinsu matasa ne masu hali da matan aure da yara da suke yawo a titunan Kano tun safe har dare.

“Babban abin da ke damunmu shi ne yadda wasun su ke amfani da shi wajen fakewa da aikata munanan dabi’u kamar karuwanci da sace-sacen waya.

“Suna kwana a gine-ginen da ba a kammala ba, shagunan kasuwa da kuma karkashin gadoji.

“Wasu daga cikin matan ma an yi masu ciki, yayin da wasu daga cikinsu motoci suke bige su lokacin bara.

“Mun mayar da wadanda ba ‘yan Kano ba ne zuwa jihohinsu, yayin da ’yan Kano suka dawo da iyalansu.

“A cikin adadin da aka kama, 611 mata ne da maza 211. Mun dawo da mata 573 da maza 278, daga cikinsu 53 sun fito daga wasu jihohi.”

Sai dai ya ce,  mabaratan da aka kama fiye da sau daya za a gurfanar da su gaban kuliya.

Kwamandan ya kuma ce, yara mabarata, wadanda ba a iya tantance iyalansu ba za a shigar da su makarantu.