✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana dab da fara cinikin filin jirgin saman Abuja, Kano da wasu guda 2

Sai dai za a fara ainihin cinikin ne a watan Fabrairun 2022.

Gwamnatin Tarayya za ta fara gayyatar kamfanonin gida da na ketare da suka cancanta a watan Yuni domin fara cinikin manyan filayen jiragen sama guda hudu.

Ministan Harkokin Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika wanda ya bayyana hakan ya kuma ce za a fara ainihin cinikin ne a watan Fabrairun 2022 lokacin da Majalisar Zartarwa ta Kasa za ta kammala nazari a kan masu bukatar sayen filayen.

Filayen da lamarin zai shafa dai sun hada da na Murtala Muhammed da ke Legas, na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja da na Malam Aminu Kano da ke Kano da kuma na Fatakwal da ke Jihar Ribas.

Ministan ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, lokacin da yake jawabi kan matakan sayar da filayen yayin Taron Cinikayyar Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Abuja.

Ya ce tsawon shekara shida kenan gwamnati mai ci na kokarin sayar da filayen amma ba ta sami damar yin haka ba saboda tana son ta bi lamarin sau da kafa.

Hadi Sirika ya ce duk da irin sukar da lamarin ke sha, babu gudu babu ja da baya a aniyar gwamnatin tasu.

Ya kuma ba da tabbacin cewa babu ma’aikacin Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) ko guda daya da zai rasa aikinsa sakamakon cinikin.

Ya ce, “Idan ko mutum daya na fahimci zai rasa aikinsa ta sanadin wannan cinikin, zan dakatar da shi baki daya.

“Matukar mu ne muka dauke ka aiki, ka cancanta kenan kuma babu abin da zai sa ka rasa aikin naka. A zahirin gaskiya ma sai mun bukaci karin ma’aikata nan ba da jimawa ba,” inji Ministan.