✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da zawarcin ’yan wasan kwallon kafa

Ana ci gaba da hada-hada a bangaren saye da sayarwa da kuma zawarcin ’yan wasan kwallon kafa,  a daidai da kakar sayar da ’yan wasan…

Ana ci gaba da hada-hada a bangaren saye da sayarwa da kuma zawarcin ’yan wasan kwallon kafa,  a daidai da kakar sayar da ’yan wasan take gudana a sassan duniya.
kungiyoyin Ingila da dama suna ta kai-komo wajen cefano ’yan wasa daga wasu kungiyoyin domin karfafa nasu kafin a fara fafatawa a kakar wasa mai zuwa.
Tuni kungiyar kwallon ta Arsenal da ke kasar Ingila ta sayo dan wasan kasar Japan mai suna Takuma Asano mai shekara 21, yayin da zakaran gasar Premier ta Ingila ta bana, Leicester City ta nuna sha’awarta ta na sayen Nempes Mendez, mai shekara 24 don buga mata wasa na tsawon shekara hudu.
 Manchester United ta Ingila tana dab da sayen dan wasan Kuroshiya, Herik mai shekara 25 kuma ta bayyana niyyarta ta sayen dan wasan Swedeen Zlatan Ibrahimobic a matsayin kwantaragi na tsawon shekara daya.
kungiyar Chelsea kuma, ta kammala sayen dan wasan kasar Beljiyum Mudingayi mai shekara 22.