Kotu ta yanke wa wani mutum hukuncin zaman gidan yari na wata tara kan laifin satar doya ƙwara biyu.
A ranar Alhamis Kotun Majistare da ke Kafanchan, Jihar Kaduna, ta yanke masa hukuncin, bayan ya amsa cewa yunwa ce ta sa shi satar doyan, ya kuma nemi sassauci.
Alkalin kotun, Michael Bawa, ya ba wa mutumin zaɓin biyan tarar N50,000 ko zaman gidan yari na wata tara.
- Yadda jama’ar gari suka kashe ’yan fashin daji 37 a Zamfara
- Ba ta yi barci ba a shekara 30
- Mai shayi ya kashe saurayi saboda taliyar yara a Jigawa
Tun da farko jami’in Sibil Difens mai gabatar da ƙara, Marcus Audu, ya shaida wa kotun cewa, a ranar 15 ga watan Agusta ne mutumin ya shiga gonar mai ƙara, Alice Daniel, ya saci doya ƙwara biyu a yankin Zonkwa.
(NAN)