✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗaure mutum 6 shekaru 120 kan satar yara a Kano

Alƙalin kotun ta ce an same su da laifin daban-daban wanda hakan ya sa aka yi musu hukunci.

Wata Babbar Kotu a Jihar Kano, ta yanke wa wasu mutum shida hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekaru 120, bisa samun su da laifin satar yara da kuma sayar da su.

Mutanen da aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Mercy Paul, Ebere Ogbono, Emmanuel Igwe, Loise Duru, Monica Oracha, da Chinelo Ifedigwe.

An same su da laifin ɓoye bayanai, taimakawa wajen aikata laifi, satar yara da kuma safarar su.

An sace yaran ne daga Kano, sannan aka sayar da su a garin Onitsha da ke Jihar Anambra.

Shugaban tawagar, Paul Onwe, tuni aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 104 a gidan yari a watan Yulin 2021, bayan ya amsa laifuka 38 da ake zarginsa da aikatawa.

Amma sauran mutanen shida sun musanta laifin, shi ya sa aka gurfanar da su a gaban kotu domin shari’a.

Alƙalin da ta jagoranci shari’ar, Mai Shari’a Zuwaira Yusuf, ta ce an same su da laifi kuma ta yanke musu hukunci daban-daban ba tare da zaɓin biyan tara ba.

Mercy Paul ta samu hukuncin ɗaurin shekaru 55 a gidan yari, Ebere Ogbono shekaru 41, Emmanuel Igwe shekaru tara, Loise Duru shekaru shida, Monica Oracha shekaru biyar, sai Chinelo Ifedigwe shekaru tara.

An kama su ne tun a shekarar 2019.

Bayan shekaru shida ana shari’a, an kammala shari’ar.

Wannan lamari ya jawo hankalin jama’a sosai tare da nuna irin hatsarin safarar yara da ke ƙara yawaita a Najeriya.