✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ɗaure mutum 1000 saboda zanga-zangar yunwa — Amnesty

Ƙungiyar ta koka kan yadda hukumomi a Najeriya suka take haƙƙin ɗan Adam yayin zanga-zangar.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan Adam ta Amnesty International, ta bayyana cewa fiye da mutum 1,000 da suka yi zanga-zangar yunwa aka tsare a gidajen yari daban-daban a Najeriya.

Ƙungiyar, ta zargi gwamnatin Nijeriya da ƙara matsa wa masu zanga-zangar lumana lamba ta hanyar gurfanar da fiye da 1,000 a kotu.

Aminiya, ta ruwaito yadda aka faro zanga-zangar a ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta ta rikiɗe zuwa tashin hankali a wasu jihohi.

A ranar 6 ga watan Agusta, Sufeta-Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bayyana cewa ‘yan sanda sun kama wasu daga cikin waɗanda suka ɗauki nauyin tada tarzoma, ciki har da waɗanda suka ɗauki nauyin ɗinka tutar Rasha.

A ranar Juma’a, Amnesty International ta sanar shafinta na X, cewa akwai buƙatar a saki dukkanin waɗanda aka kama saboda yin zanga-zangar lumana ba tare da wani sharaɗi ba.

Ƙungiyar ta ce, “Gwamnatin Najeriya tana ƙara tsananta wa waɗanda suka yi zanga-zangar lumana kan yunwa.

“Sama da mutum 1,000 aka tsare a dukkanin faɗin ƙasar. A yau, an gurfanar da mutum 441 a kotun Kano, a wasu shari’o’i na rashin adalci da aka yi bisa tuhume-tuhumen ƙarya.‚

Amnesty International, ta kuma tunatar da gwamnatin Najeriya wajibcin kare haƙƙin ‘yancin faɗin albarkacin baki da kuma yin zanga-zangar lumana.