Wata Kotun Majistare da ke yankin Isabo a Abeokuta, ta yanke wa wani matashi mai suna Kazeem Salami, hukuncin ɗaurin shekara ɗaya a gidan gyaran hali bisa samunsa da laifin satar kayan abinci da kuɗinsu ya kai Naira 1000.
Alkalin kotun Misis V.B. Williams, ta ce masu gabatar da ƙara sun tabbatar da hakan ba tare da wata shakka ba, inda ta ƙara da cewa hakan ne ya sanya aka yanke wa matashin hukunci kan laifin da ake tuhumarsa.
- CAF ta sanya ranar da za a fara gasar AFCON ta 2025
- Gwamnatin Kano ta ba da umarnin fitar da Sarki Bayero daga Fadar Nassarawa
Kamfanin Dillancin Labarai (NAN), ya ruwaito cewa matashin ya ƙi amsa laifin da ake tuhumarsa da shi a gaban kotun.
Tun da farko, mai gabatar da ƙara, Lawrence Olu-Balogun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 5 ga watan Maris.
Ya ce an aikata laifin ne da misalin ƙarfe 3:00 na dare, a titin Duroja da ke ƙauyen Ake kusa da Laderin a Abeokuta.
Mai gabatar da ƙara ya bayyana cewa mazauna unguwar ne suka hangi wanda ake tuhumar yana satar kayan abincin.
Kazalika, ya ce matashin ya kasa kare kansa bayan shiga hannun jami’an tsaro a jihar.
A cewarsa, wanda aka yanke wa hukuncin ya kasa bayyana inda ya samo kayan abincin da yake ɗauke da su wanda kuɗinsu ya kai Naira 1000.
Mai gabatar da ƙara ya ce laifin ya ci karo da sashe na 390 (9) na kundin dokokin Jihar Ogun na shekarar 2006.