Tun bayan da aka samu sabani tsakanin Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko da Sanata Ibrahim Lamido, lamarin ya zafafa inda kowannensu ya ware tare da magoya bayansa.
Duk da kasancewarsu a jam’iyya daya ta APC, adawa ta yi tsanani tsakanin jagororin biyu.
- Sadaukarwar ’yan Najeriya ba za ta tafi a banza ba — Tinubu
- Kasafin 2024 zai kai watan Yunin 2025 – Akpabio
Wasu magoya bayan Sanata Lamido, suna ganin matakan da yake dauka suna da kyau, tare da fatan cewa zai samu nasara.
Honarabul Buhari Shaikh Sidi Attahiru, ya ce Lamido yana kokarin cika alkawuransa ga al’umma, kuma hakan zai ja masa nasara daga Allah.
Ya yi misali da lokacin da Wamakko ya ci zaben gwamna duk da rashin goyon bayan manyan jam’iyyar a lokacin.
A daya bangaren, wasu masu sharhi na ganin Sanata Lamido na kokarin barin APC ne, shi ya sa yake rikici da jagororinta.
Sun ce ba zai yiwu ba a ce uwar jam’iyya ta kasa ta dauki Lamido wanda ke son neman takardar gwamna, ta bar gwamna mai ci da ministoci biyu a gefe.
A karshen makon da ya gabata, Sanata Lamido ya hadu da Alhaji Sa’idu Umar Ubandoma, dan takarar gwamna na PDP a 2023, a wajen daurin aure.
Daga baya kuma sun gana a gidan dan majalisa Bello Isah Ambarura, inda suka yi liyafa tare da tattaunawa.
Wannan hulda ta sa mutane suna hasashen cewa Lamido zai koma PDP.
A Facebook, mataimaki na musamman ga Sanata Wamakko, Bashar Abubakar, ya yi shagube inda ya ce, “‘Yan aware sun fara nuna alkiblarsu!.”
Mataimakin Sanata Lamido, ya mayar da martani cewa, “Mu fa Allah kadai muke tsoro.”
Wakilinmu ya yi kokarin tuntubar Sanata Lamido domin karin bayani, amma bai samu damar magana da shi ba.