✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi wasu sarakuna da bayar da mafaka ga miyagun mutane a masarautunsu

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo Mista Shina Olukolu ya gargadi wasu Sarakuna da ake zargi da bayar da mafaka ga masu garkuwa da mutane…

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Oyo Mista Shina Olukolu ya gargadi wasu Sarakuna da ake zargi da bayar da mafaka ga masu garkuwa da mutane a masarautunsu da su hanzarta janye jikinsu daga wannan mummunan aiki tun kafin mahukunta su yi masu dirar mikiya. Kwamishinan ya yi wannan gargadi ne a Ibadan a ranar Asabar da ta gabata a wajen wani taro na musamman da ya yi tare da Sarakunan garuruwan yankin Oke-Ogun da suka yi kusa da kan iyakar Najeriya da kasar Benin. ‘Bayanan da muke samu sun nuna cewa, wasu daga cikin ku (sarakuna) a wannan yanki na Oke-Ogun suna amincewa miyagun mutane musamman masu garkuwa da mutane samun matsuguni a cikin masarautunsu bayan sun gudo daga wasu sassa na Arewacin kasa da suka aikata danyen aikin na su.’ Kwamishinan ya yi kira ga irin wadannan shugabannin al’umma da su dawo daga rakiyar wannan mummunan aiki da ya kasance barazana ga tsaron kasa. Yace, ’kamata ya yi kowane Sarki ya fito ya nuna kishin kasa wajen bayar da gudunmawar da za ta taimaka ga tabbatar da tsaron lafiyar al’ummarsa a maimakon hada baki da miyagun mutane domin tayar da zaune a masarautarsa. Ya tunatar da sarakunan da ake zargi a kan lamarin cewa ‘idan al’amarin ya kazance to da hannunku a ciki. Saboda haka wajibi ne kowane Sarki ya dauki matakin tsaftace masarautarsa ta hanyar sanya ido da kyakkyawar lura ga bakin mutane masu shigi da fici a cikin masarautunsu da ya kamata a rinka tantance su kafin a basu matsuguni.” Wasu sarakuna da suka hada da Aare na Ago-Are Oba (Dakta) Kofoworola Oyetunji da Alagere na Ofiki Oba Basiru Oyesiji da Olowode na Irawo-Owode Oba Jibril Adetunji Adeleke sun yi jawaban kare kai dangane da wannan zargi, a inda suke cewa, ‘sarakunan yankin Oke-Ogun suna yin taro kusan sau 2 a cikin wata daya domin tattaunawa a kan samo mafita a kan tsaron lafiyar al’umma. Muna so Kwamishinan ‘yan sanda ya bayyana sunan dukkan Sarkin da suke zargi da hannu a kan wannan al’amari.’ Jawaban wasu sarakunan kuwa sun dora alhakin zargin ne a kan Kungiyar Miyetti Allah wanda a nan take da Shugaban Kungiyar ta Miyetti Allah a Karamar Hukumar Atisbo. Alhaji Salihu Muhammed ya tashi ya kare kungiyarsa da mutanensa cewa, ’Muna goyon bayan matakin da ’yan sanda suke dauka a kan wannan al’amari. Ina so masu zarginmu su gane cewa a matsayin mu da muka shafe shekaru fiye da 50 zaune a wannan yanki na Oke-Ogun babu yadda za mu goyi bayan ayyukan ta’addanci. ‘Yan kwanaki kadan da wucewa kenan da irin wadannan ’yan bindiga suka kashe dan uwan Sarkin Fulanin Tede kuma har yanzu ba a yi mana maganin shanun da ake sace mana ba.