✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi kamfanin Birtaniya da yin kasalandan a zaben shekarar 2007

  Gidan Rediyon BBC ya ruwaito cewa kamfanin kididdiga da tattara bayanai mai suna Cambridge Analytica ya yi ikirarin yin kasalandan a kasashe waje har…

 
Gidan Rediyon BBC ya ruwaito cewa kamfanin kididdiga da tattara bayanai mai suna Cambridge Analytica ya yi ikirarin yin kasalandan a kasashe waje har da Najeriya.
 
Kamfanin ya shiga tsaka mai wuya kan zargin da ake yi masa na juya bayanan miliyoyin masu amfani da kafar sa da zumunta ta Facebook.
 
Gidan rediyon BBC ya ga wasu takardu da jigon kamfanin mai suna SCL ya buga kafin zaben 2014 inda suka nuna cewa kamfanin ya shirya zanga-zanga don ya rage karfin ’yan adawa a kasar.