A ranar Talatar da ta wuce ne Kwamitin ladabtarwa na Hukumar da ke kula da gasar rukuni-rukunin Najeriya (NPFL) ya bayar da sanarwar zaftare wa kulob din Giwa FC na garin Jos maki uku saboda rashin halartar wasa a tsakanin kulob din da na Wikki Tourist Bauchi a ranar Lahadin da ta wuce a garin Ilorin.
Shi dai kulob din Giwa ya ki halartar wasan ne ba tare da wani kwakkwaran dalili ba da hakan ya sa kwamitin ya zaftare masa maki uku daga makin da ya hada a teburin gasar.
Kwamitin ya ce bayan an zaftare wa kulob din Giwa maki uku ne sai aka kara wa na Wikki Tourist maki uku da kwallaye uku da hakan ta sa kulob din na Wikki ya koma matsayi na biyar a teburin gasar da maki 22 yayin da na Giwa FC ya koma matsayi na 14.
Idan za a iya tunawa kulob din Giwa FC da ke garin Jos dai ya ki halartar wasa ne a tsakaninsu da Wikki Tourist na Bauchi a gasar rukunin Najeriya da yakamata a yi a Ilorin bayan an dage kulob din daga yin wasanninsa na gida a Jos zuwa Ilorin saboda rashin da’ar da magoya bayansa suka nuna a wasansu da na Enugu Rangers a garin Jos a makon jiya.
Tun daga wancan lokaci ne kulob din FC Giwa ya daina halartar wasanninsa na gida a Ilorin da hakan ya nuna watakila a dage kulob din daga gasar saboda nuna rashin da’a.
An zaftare wa kulob din Giwa FC maki uku
A ranar Talatar da ta wuce ne Kwamitin ladabtarwa na Hukumar da ke kula da gasar rukuni-rukunin Najeriya (NPFL) ya bayar da sanarwar zaftare wa…