✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi ‘yar Najeriya cikin ’yan jaridar duniya da za su samu horo na musamman

An zabi ’yar Najeriya, Fauziyya Kabir Tukur,  cikin ’yan jarida 10 daga kasashen duniya da za su halarci wani shiri na musamman na samun karin…

An zabi ’yar Najeriya, Fauziyya Kabir Tukur,  cikin ’yan jarida 10 daga kasashen duniya da za su halarci wani shiri na musamman na samun karin kwarewa badi a Amurka.

Shirin, wanda Cibiyar Inganta Aikin Jarida ta Duniya (WPI) ke shiryawa, shi ne irinsa na 58.

Wadannan ’yan jarida 10 “za su shafe makwanni tara suna nazari a kan ’yancin kafofin yada labarai [na bayyana gaskiya] da sababbin hanyoyin yada labarai; sannan kuma za su nazarci bambance-bambancen al’umma da al’adu a Amurka, da ma tsarin siyasar kasar”, inji Cibiyar.

Fauziyya Kabir Tukur babbar ma’aikaciya ce a bangaren yaki da labaran karya na BBC.

Kafin ta fara aiki a wannan bangare dai tana aiki ne da Sashen Hausa na BBCn a matsayin mai aika rahoto kuma mai gabatar da shirye-shirye a Abuja.

Fauziyya Kabir Tukur
Fauziyya Kabir Tukur tana jawabi yayin taron bayar da kyaututtuka ga gwarazan Hikayata bara

Ita ce kuma ta jagoranci shirya Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, a shekarar 2021.

Sauran mutane taran da za su halarci wannan horo sun fito ne daga kasashen Argentina da Australia da Brazil da Bulgaria da Finland.

Sa kuma mutum guda-guda daga Faransa da Pakistan da Sri Lanka da kuma Turkiyya.

Za a fara wannan horo ne daga watan Maris zuwa watan Mayu na 2023.

’Yan jaridar za su zaga sassa daban-daban na kasar Amurka, inda za su hadu da takwarorin aikinsu da kwararru a kudurorin gwamnati da ’yan siyasa da ’yan kasuwa da shugabanin al’umma a biranen New York da Washington DC da Miami da Austin (Texas) da Chicago da San Francisco da Los Angeles da Minnesota.

Sauran batutuwan da za a fi mayar da hankli a kansu yayin wannan horo sun hada da tsarin siyasar Amurka, musamman abubuwan da suka shafi zabe, da cibiyoyi da sauyin yanayi, da samar da abinci da kuma sababbin fasahohin aikin jarida, da sababbin dabarun kasuwanci na zamani.