A ranar Alhamis, Gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi, ya damka ragamar shugabancin Kungiyar Gwamnonin Najeriya ga takwaransa na jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal.
Taron mika ragamar dai ya gudana ne yayin Taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa da ya gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Tambuwal ya shafe shekara hudu a matsayin Mataimakin Shugaban kungiyar karkashin Fayemin.
Gwamnan na Ekiti mai barin gado ya halarci taron ne ta intanet daga birnin New York na Amurka, inda yake tare da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, inda suke halartar taron Babban Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 (UNGA-77).
Gwamnan na jihar Sakkwato dai zai ci gaba da rike mukamin na wucin gadi ne har nan da watan Mayun 2023, lokacin da Gwamnonin za su gudanar da sabon zabe.
Da yake jawabi yayin taron, Gwamna Fayemi ya gode wa takwarorinsa Gwamnonin kan irin gudunmawa da goyon bayan da suka ba shi lokacin da yake rike da Shugabancin kungiyar.
A ranar 16 ga watan Oktoba ce dai ake sa ran Fayemi zai mika ragamar shugabancin kungiyar a hukumance ga Gwamna Tambuwal.