✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Shugaban NFF a kwamitin shirya gasar cin kofin Afirka

Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta zabi Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa watau NFF Mista Amaju Pinnick a matsayin daya daga…

Hukumar shirya kwallon kafa ta Afirka (CAF) ta zabi Shugaban Hukumar shirya kwallon kafa ta kasa watau NFF Mista Amaju Pinnick a matsayin daya daga cikin ’yan kwamitin da za su kula da yadda gasar za ta gudana a kasar Ekuatorial Guinea a watan Janairu mai zuwa.
A wata takarda mai dauke da sanya hannun shugaban CAF Issa Hayatou da aka aiko wa Hukumar NFF ta nuna an nemi  Amaju Pinnick  ya laharci bikin bude gasar da za a fara a ranar 17 ga watan Janairun 2015 yayin da ake sa ran rufeta a ranar 8 ga Fabrairun, 2015 watau za a dauki tsawon makwanni uku ana gudanar da ita kenan.
Ana sa ran Shugaban NFF din ne zai kula da daya daga cikin shiyyoyi hudu da za a gudanar da gasar a cikinsu.
Shi dai kwamitin, shi ne kwamitin da ya fi kowane karfi wajen kula da yadda gasar ke gudana.
Idan za a tuna Najeriya ba za ta halarci gasar ba, bayan ta kasa kai bantenta a gasar neman hayewa gasar da aka fafata.