A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta zabi sabon shugabanta duk da matsalar da aka samu na raba hukumar gida biyu. Wanda wadansu daga cikin wakilan Hukumar suka zaba a matsayin sabon shugaba shi ne Mista Chris Giwa, mai kulob din Giwa FC da ke Jos.
Zaben ya gudana ne a Otel din Chida da ke Utako a Abuja.
Sai dai daya bangaren da ke adawa da zaben, wadanda ke goyon bayan tsohon shugaban Hukumar Alhaji Aminu Maigari da ake wa lakabi da “bangaren Mike Umeh” ya ce bai yarda da zaben ba, hasalima dai wadanda suka gudanar da zaben ba su yi shi a kan ka’ida ba, don tun da farko daukacin membobin Hukumar sun zartar da cewa sai a ranar 4 ga watan gobe ne za a gudanar da zaben ba a ranar 26 ga watan nan ba, don haka ba su amince da zaben sabon shugaban ba.
bangaren ’yan adawar wanda Mista Mike Umeh ya yi wa ’yan jarida bayani ya ce taron da aka yi a ranar Talata a Otel din Chida ba an shirya shi don gudanar da wani zabe ba, an shirya taron ne don a fito da hanyoyin da suka kamata a bi don a gudanar da sahihin zabe a ranar 4 ga watan gobe a garin Kalaba, amma abin mamaki sai aka wayi gari wadansu daga cikin membobin hukumar suka ce wai sun zabi sabon shugaba a taron bayan da yawansu sun kauracewa taron.
Tun da farko kafin a fara zaben, da yawa daga cikin membobin da suka halarci taron wadanda suka wakilci sassan Jihohin kasar nan sun yi mamakin rashin ganin tsohon Shugaban NFF Alhaji Aminu Maigari da ’Barista Chris Green tsohon shugaban kwamitin gudanar da tsare-tsare a Hukumar da kuma Babban Sakataren Hukumar Barista Musa Amadu. Bayan sun yi bincike ne suka gano jami’an tsaron SSS ne suka kama su kafin a fara gudanar da taron al’amarin da ya sa suka bar wurin taron suka nufi Hedkwatar hukumar da ke Maitama, Abuja.
A lokacin da wasu daga cikin membobin Hukumar wadanda ke goyon bayan Alhaji Aminu Maigari suka yi kokarin isa hedkwatar SSS da ke Abuja don jin dalilin kama musu shugabanni ba tare da wani kwakkwaran dalili ba ne suka yi artabu da jami’an tsaro na ’yan sanda inda ’yan sandan suka nemi hana su isa hedkwatar SSS din, yayin da su kuma suka kekasa-kasa sai sun isa. Daga baya ne dai aka sasanta kuma aka sako shugabannin.
Sai dai a ranar da misalin karfe 6 da kwata na yamma ne Ministan wasanni Dokta Tamuno Danagogo tare da daya daga cikin wadanda hukumar SSS ta kama Barista Musa Amadu suka isa Otel din Chida inda ya yi wa mahalarta taron jawabi.
Ya ce ya san an samu bangarori biyu a Hukumar wanda yin haka ya zama abin takaici. Ya ce su sani cewa zaben shugaban Hukumar NFF kada ya zama wani abin a-mutu-ko-a-yi rai kamata ya yi a bi komai cikin natsuwa don kada a jawo wa Najeriya matsala a sha’anin wasanni.
Daga nan ne ya gabatar da wasikar ajiye mukamin da tsohon shugaban Hukumar Alhaji Aminu Maigari ya yi. Da aka tambaye shi dalilin da ya sa bai bayyana wasikar yin murabus din tsohon shugaban ba sai a ranar, Ministan ya ce ya yi haka ne saboda da daga ranar ce takardar ajiye aikin tsohon shugaban za ta fara aiki don haka shi bai ga wani laifi a kan hakan ba.
A nasa bangaren, sabon shugaban Hukumar da aka zaba Mista Chris Giwa ya ce ya gode wa Allah a kan yawan kuri’un da ya samu na 27 bayan ya doke abokin takararsa Cif Mike Umeh da ya samu kuri’u biyu.
Ya ce zai yi kokarin ganin ya hada kan membobin hukumar don cigaban hukumar da ma Najeriya baki daya.
Sai dai duk kokarin da manema labarai suka yi don jin ta bakin tsohon shugaban Hukumar Alhaji Aminu Maigari a kan wannan dambarwa abin ya ci tura ya zuwa lokacin hada wannan rahoto.
An zabi sabon Shugaban Hukumar NFF bayan ta dare gida biyu
A ranar Talatar da ta wuce ne Hukumar shirya kwallon kafa ta Najeriya (NFF) ta zabi sabon shugabanta duk da matsalar da aka samu na…