Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Jihar Delta Mista Amaju Pinnick ne aka zaba a matsayin sabon shugaban Hukumar NFF a ranar Talatar da ta gabata a garin Warri da ke Jihar Delta.
Amaju Pinnick zai jagoranci Hukumar har na tsawon shekara hudu kenan bayan wa’adin tsohon shugaban hukumar Alhaji Aminu Maigari ya kare.
Sai dai an gudanar da zaben har sau biyu ne kafin Pinnick ya samu nasara. A zagayen farko Amaju Pinnick ya samu kuri’u 29 daga cikin kuri’u 44 da membobin hukumar suka kada amma hakan bai ba shi damar samun kashi biyu daga cikin uku na yawan kuri’un da ake bukata kafin a lashe zaben ba. Hakan ta tilasta sake kada kuri’u a zagaye na hiyu inda ya samu kuri’u 32 yayin da wadanda suka fafata da shi watau Dominic Irofa ya samu kuri’u takwas shi kuma Taiwo Ogunjobi ya samu hudu.
Kimanin ’yan takara shida ne suka fafata da suka hada da shi kansa Amaju Pinnick da Dominic Iorfa da Taiwo Ogunjobi da Uchegbulam Amanze da Abba Yola da kuma Mike Umeh. Sai dai daya daga cikin ’yan takatar shugabancin Hukumar Shehu Dikko bai samu halartar zaben ba saboda wani rahoto da aka samu cewa jami’an tsaron farin kaya SSS sun yi garkuwa da shi a Abuja.
Sannan an samu labarin jami’an tsaro sun yi ram da Shugaban Kwamitin shirya zaben Samson Ebohme kafin a fara gudanar da zaben amma sai daga baya sun sake shi.
A wani labari makamancin wannan, Chris Giwa wanda aka zaba a matsayin Shugaban Hukumar NFF a ranar 26 ga watan Agustan wannan shekara a Abuja ya bayyana cewa bai amince da zaben Warri ba kuma ya yi niyyar shiga ofis a jiya Alhamis don fara gudanar da aiki bayan da wata kotu a Jos ta bayar da umarnin a rantsar da shi a matsayin shugaban Hukumar.
Mista Chris Giwa ya ce a matsayinsa na shugaban da aka zaba a ranar 26 ga watan Agustan wannan shekara, bai yarda da sabon zaben da ya gudana a Warri a ranar Talatar da ta gabata ba, don haka shi ne dai sabon shugaban Hukumar NFF.
Wannan yunkuri da Giwa yake naman yi, na iya kawo cikas a dambarwar da ke faruwa a Hukumar ta NFF.
Sai dai daya daga cikin wadanda suka tsaya takarar Alhaji Abba Yola ya amince da zaben da ya gudana a Warri inda ya nuna an yi zaben cikin ka’ida ba tare da magudi ba. Don haka bai amince da ikirarin da Giwa yakew yi na cewa shi ne sabon Shugaban Hukumar ba.
Sauran shugabannin da aka zaba a matsayin ta-zarce sun hada da Barista Christopher Green da Cif Agwu Felid Anyansi da Alhaji Ahmed Yusuf Fresh da kuma Honorabul Suleiman Yahaya Kwande. Shugaban Hukumar FA ta Jihar Legas Seyi Akinkumi ne aka zaba a matsayin Mataimakin Shugaba.
Haka kuma an zabi Shugaban Hukumar FA ta Zamfara Musa Gusau Ibrahim ba tare da hamayya ba a matsayin shugaban kwamitin kwamitoci yayin da aka zabi Ahlan Sheriff Inuwa daga Jihar Kano a matsayin memba da ya fito daga yankin Arewa maso Yamma.
Shi kuma Shugaban Hukumar FA ta Ondo Sunday Dele Ajayi ne aka zaba daga yankin Kudu maso Yamma yayin da aka zabi Shugabannin Hukumar FA ta Taraba da na Jihar Borno Alhaji Modibbo Hussaini wadanda za su wakilci yankin Arewa maso Gaba a Hukumar.
An gudanar da zaben lafiya kuma an tashi lafiya ba tare da wata hatsaniya ba.
A jawabin sabon shugaban Mista Amaju Pinnick ya sha alwashin hada kan membobin Hukumar ta NFf don a samu cigaba mai dorewa.
An zabi sabon Shugaban Hukumar NFF
Shugaban Hukumar kwallon kafa ta Jihar Delta Mista Amaju Pinnick ne aka zaba a matsayin sabon shugaban Hukumar NFF a ranar Talatar da ta gabata…
