Majalisar masu unguwannin garin Jos da kewaye sun zabi Alhaji danlami Babanjoda a matsayin sabon sarkin Fawan Jos. Masu unguwannin sun gudanar da zaben sabon sarkin Fawan ne a ranar lahadin da ta gabata a dakin taro na babban masallacin juma’a na garin Jos. Wannan zaben sabon sarkin Fawan da masu unguwannin suka yi, ya kawo karshen takaddamar da aka yi sama da shekara 24, ana yi, kan zaben sabon sarkin Fawan.
Da yake jawabi a wajen mai girma Sarkin Narkuta Alhaji Muhammad Bello Abubakar ya bayyana cewa bisa abin da suka yi da jami’an gwamnati da jami’an tsaro sun dauki matsaya kan Alhaji danlami Babanjoda ya zama sabon sarkin Fawan Jos. A yayinda wanda suka yi takara, wato Malam Salisu Maitala ya zama Madakin sarkin Fawan Jos.
Ya yi nasiha ga Alhaji danlami Babanjoda kan ya ji tsoran Allah kan wannan jarabawa da aka yi masa, domin Allah ne Ya sa aka zabe shi a wannan sarauta.
Har’ila yau ya yi kira Malam Salisu Maitala ya yi biyayya kan wannan matsaya da aka dauka, domin shugabanci lokaci ne. Ya ce ba mamaki idan Allah ya yi masa tsawon rai wannan shugabanci yazo gareshi.
Ya yi fatar sabon sarkin Fawan zai rike kowa da kowa a wannan sarauta da aka zabe shi. Kuma ya rike mutumin da suka yi takara tare batare da muzantawa ko kaskanci ba.
Da yake zantawa da wakilinmu sabon sarkin Fawan na Jos, Alhaji danlami Babanjoda ya mika godiyarsa ga dukkan masu unguwannin cikin garin Jos da kewaye da dukkan kungiyoyin addinin musulunci dake garin Jos kan wannan zabe da aka yi masa.
Ya ce ya yafe duk abin da wadanda suka nemi wannan sarauta suka yi masa, a tsawon lokaci da aka yi, ana neman wannan sarauta. Don haka ya yi kira kan su bashi goyan baya da hadin kai.
‘’Ni yanzu kowa nawa ne a wannan sana’a ta fawa a Jihar Filato baki daya. Don haka ina kira ga dukkan mahautan Jihar Filato su ji tsaron Allah kan wannan sana’a su gyara wannan sana’a’’.