Wasu mazauna jihar Katsina a ranar Asabar sun yi kaiwa da kawo wa a kan wasu hanyoyi na jihar inda suka gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadi dangane da harin da ’yan bindiga suka kai wata makarantar kwana ta gwamnati ranar Juma’a a garin Kankara.
Masu zangar-zangar karkashin jagorancin wata mata da ta bayyana kanta a matsayi daya daga cikin iyayen daliban, sun nemi a ceto daliban makarantar ta maza zalla, GSSS Kankara da ’yan bindigar suka yi awon gaba da su.
- Boksin: Buhari ya jinjina wa nasarar Anthony Joshua
- Za a gina wa malaman makaranta gidaje 5,000 a Kano
Aminiya ta ruwaito cewa an yi zanga-zangar ne a harabar makarantar da kewayenta da kuma wasu sassa na garin Kankara dauke da alluna gami da yin wake da ambaton Gwamnati ta fito ta yi magana, ‘Muna son a ceto yaranmu’, da sauran sakonni na samar wa da al’umma tsaro.
Ana tsammanin ’yan bindigar sun yi awon gaba da daruruwan dalibai yayin harin da suka kai makarantar cikin duhun dare haye a kan Babura kimanin 150.
A ranar Asabar ne mai magana da yawun Shugaban Kasa Mallam Garba Shehu ya sanar cewa, jami’an tsaro na soji sun gano maboyar ’yan bindigar a Kankara kuma an yi musayar wuta da su.